Sakataren APC Ya Fadi Abin da Ya Taimaki Bola Tinubu, Ya Doke Atiku Abubakar da Obi

Sakataren APC Ya Fadi Abin da Ya Taimaki Bola Tinubu, Ya Doke Atiku Abubakar da Obi

  • Sakataren APC a Najeriya yana ganin babu magudi da murdiyar da Bola Tinubu ya yi a zaben 2023
  • Iyiola Omisore ya shaida cewa hankali kwance APC ta samu nasara, saboda karbuwar Bola Tinubu
  • Sanata Omisore yace rikicin cikin gida da rashin hadin-kai ya Hana Jam’iyyun hamayya su kai labari

Abuja - Babban Sakataren APC na kasa, Iyiola Omisore ya yi bayanin abin da ya taimakawa Bola Ahmed Tinubu a zaben 25 ga watan Fubrairun 2023.

The Nation ta rahoto Sakataren jam’iyyar APC yana cewa yadda Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya samu kuri’u daga kowane bangare ne ya ba shi nasara.

Sanata Iyiola Omisore yace bazuwar kuri’un ‘dan takaran na APC ya nuna yadda ya karbu sosai, sannan ya dage wajen hada-kai da al’ummar kasar.

Tsohon mataimakin Gwamnan na jihar Osun ya na cikin masu ganin ba ayi magudi a zaben 2023 ba, yana mai watsi da wadanda ke ikirarin an yi murdiya.

Kara karanta wannan

Mun kadu: Atiku da Tinubu sun yi gamin baki, sun yi jajen hadarin da ya faru a Legas

Omisore ya ce ba ayi magudin zabe ba

Omisore ya ce an san duk wanda ya sha kashi a zabe da yin koke-koke da nuna an yi ba daidai ba saboda kokarin bata kima da darajar zaben adalcin da aka yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jagoran na jam’iyya mai ci ya soki jam’iyyun hamayya na PDP da LP da suka zo na biyu a zaben shugaban kasar da amfani da son rai wajen nazarin zaben.

Tinubu
Buhari da Bola Tinubu a Katsina Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Tsohon Sanatan na Osun yana mai mamakin yadda ‘yan adawar suka yi watsi da abin da ya faru a inda suke da karfi, suka damu da inda APC tayi galaba.

An rahoto Omisore yana cewa ba za ta yiwu a ce an yi murdiya a zaben da shugaban kasa, shugaban jam’iyya, darektan kamfe da ‘dan takara suka sha kasa ba.

A cewar Omisore, nasara ta samu ne a sakamakon goyon bayan Muhammadu Buhari, jajircewar shugabanni, hadin-kan ‘ya ‘yan APC da taimakon ‘yan kasa.

Kara karanta wannan

Sai Da Na Dage Da Addu'a Don Kawai Allah Ya Ba Tinubu Nasara, Gwamnan APC Ya Magantu

A yayin da jam’iyya mai-ci ta taki wannna sa’a, Sakatarenta ya ce LP da PDP sun shiga zabe a wargaje, baya ga haka Gwamnoni biyar suna rikici da Atiku.

Kasar Sin ta taya APC murna

‘Dan siyasar ya yi magana da manema labarai a garin Abuja, jim kadan bayan ya karbi wasikar Shugaban kasar Sin, Xi Jinping yana mai taya APC murna.

Jakadan Sin a Najeriya, Cui Jianchun ya kawowa Sakataren na APC takardar, ya karba a madadin jam’iyyar mai-ci da ‘dan takaran ta ya doke PDP da LP.

Hon. Johnson Fatoki ya bar PDP

Ku na da labari lamari ya jagwalgwalewa 'dan takaran PDP a 2023, Atiku Abubakar yayin da wanda ya amince masa a zaben 2023 ya canza gida.

Hon. Johnson Fatoki wanda aka tura a matsayin Wakilin Jam’iyyar PDP a jihar Ogun ya shiga APC, yana goyon bayan tazarcen Gwamna Dapo Abiodun.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari Ya Fayyace Komai Bayan An Ga Babu Sunansa Cikin Lauyoyin Tinubu

Asali: Legit.ng

Online view pixel