Nwosu: Za a Fara Zaman Makoki a APC, Shugaba a Jam’iyya Ya Rasu a Asibiti

Nwosu: Za a Fara Zaman Makoki a APC, Shugaba a Jam’iyya Ya Rasu a Asibiti

  • Jam’iyyar All Progressives Congress ta rasa Sakataren jin dadi da walwalarta a Najeriya
  • Friday Nwosu ya na ta jinya kwanakin baya, amma a makon nan aka sallame shi daga asibiti
  • Bayan komawa ganin likita a asibitin Abuja sai ciwo ya tashi, ana cikin haka sai ya rasu

Abuja - An tabbatar da mutuwar babban jami’in kula da walwala na jam’iyyar APC na kasa, Friday Nwosu a yammacin ranar Alhamis.

Sun ta ce Friday Nwosu wanda yana cikin ‘yan majalisar gudanarwa na NWC ya rasu ne bayan ya yi fama da ‘yar gajerar rashin lafiya.

Nwosu yana cikin jagororin PDP a Abia har ya nemi takarar kujerar Gwamna a karkashin jam’iyyar, kafin ya sauya-sheka zuwa PDP.

Masanin shari’ar ya kwanta a wani asibiti a birnin tarayya Abuja a kwanan baya, amma a ranar Laraba da ta wuce aka sallame shi.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Fitaccen sarki a Arewa ya yanki jiki ya fadi matacce a hanyar sallar Magriba

Daga komawa ganin Likita

Blueprint ya ce Nwosu ya je asibitin ranar Alhamis ne domin likitoci su duba shi, kwatsam sai aka ji cewa rashin lafiya ya kifar da shi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A nan take aka garzaya da ‘dan siyasar zuwa sashen bada agajin gaggawa, a nan ya rasu.

'Yan APC
Taron APC Hoto: www.yemiosinbajo.ng
Asali: UGC

Wata majiya ta shaida cewa mutuwar wannan ta’aliki ta gigiza jam’iyyar da daukacin ‘yan majalisar gudanarwar Abdullahi Adamu.

Ana tunanin zuwa safiya ne Shugaban APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu zai sanar da al’umma wannan rashi da jam’iyya mai-ci tayi.

Kafin ya fara rashin lafiya, Nwosu ya kira taron manema labarai a farkon Fubrairu, ya nemi Uche Ogah da Ikechi Emenike su sasanta a Abia.

Har zuwa lokacin da muke tattara rahoton nan, gawar Marigayin ta na asibitin na garin Abuja.

Kara karanta wannan

Mun kadu: Atiku da Tinubu sun yi gamin baki, sun yi jajen hadarin da ya faru a Legas

Sarkin Yaba ya cika

A daren yau ne aka ji labari Sarkin Yaba, Abdullahi Adamu ya gamu da ajalinsa yana cikin fadarsa a garin Yaba ba tare da rashin lafiya ba.

Sarkin yana fadi, fadawa suka sa shi a mota, aka tafi asibiti inda aka tabbatar da ya rasu, za ayi masa sallar jana’iza da karfe 9:00 na safe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel