Atiku da Tinubu Sun Tura Sakon Ta’aziyya Ga Ahalin Wadanda Hadarin Jirgi Ya Rutsa Dasu a Legas

Atiku da Tinubu Sun Tura Sakon Ta’aziyya Ga Ahalin Wadanda Hadarin Jirgi Ya Rutsa Dasu a Legas

  • Bola Ahmad Tinubu ya mika sakon ta’aziyya ga ahalin wadanda suka rasa rayukansu a hadarin da ya auku a Legas
  • Hakazalika, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya mika irin wannan ta’aziyya garesu
  • An samu aukuwar mummunan hadarin da ya yi sanadiyyar mutane shida a Legas a ranar Alhamis 9 ga watan Maris

Najeriya - Zababben shugaban kasa a Najeriya, Bola Ahmad Tinubu ya siffanta hadarin jirgin kasan da ya faru a Legas da yanayi mai tada hankali, PM News ta ruwaito.

Da safiyar yau Alhamis 9 ga watan Maris ne wani jirgin kasa ya yi karo da wata mota bas dauke da ma’aikatan gwamnan jihar Legas, inda shida daga ciki suka mutu.

Wani ganau ya shaida cewa, lamarin ya faru ne a lokacin riban bas din ke kokarin tsallaka titin jirgin kasan bai san jirgin na tafe ba.

Kara karanta wannan

Saura kiris zaben gwamna: Sojoji sun kama katin zabe 1,671 da takardun aikin zabe a wata jiha

Atiku da Tinubu sun yi jaje
Hadarin Legas da ya faru ranar Alhamis | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Tinubu ya bayyana rashin jin dadinsa

A cikin wata sanarwar da Tinubu ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa, Tunde Rahman, zababben shugaban ya ce zai ci gaba da bibiyar lamarin don gano hanyar da zai bi wajen taimakawa a inda ya dace.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa:

“Ina mika matukar jajantawa ga wadanda lamarin ya rutsa dasu da kuma iyalansu bisa aukuwar wannan lamari na karon jirgin kasa da bas a Ikeja da ke Legas da safiyar yau.
“Ina addu’a garesu duka, ciki har da wadanda suka mutu da wadanda suka samu raunuka a wannan hadari mara dadin ji.”

Atiku ya mika sakon jaje

A bangarensa, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubukar ya shi ma ya mika sakon ta’aziyya kan aukuwar wannan lamari mara dadi, rahoton TheCable.

Hakazalika, ya taya iyalai da wadanda lamarin ya rutsa dasu jajen abin da ya faru tare da yin addu’o’i.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari Ya Fayyace Komai Bayan An Ga Babu Sunansa Cikin Lauyoyin Tinubu

A bangare guda, ya shawarci jihohi da su mai da hankali ga ci gaban fannin sufuri, inda ya kara da cewa, ya kamata a mai da hankali kuma ga kawo agajin gaggawa.

Idan baku manta ba, rahotanni a baya sun bayyana yadda aka yi asarar rayuka bayan hadarin da ya auku a Legas.

Legit.ng ta samo cewa, a lokacin ana ci gaba da aikin tabbatar da an ceto sauran mutanen da ke cikin motar

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel