Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un: Allah Ya Yiwa Basaraken Abuja, Etsu Na Yaba Rasuwa

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un: Allah Ya Yiwa Basaraken Abuja, Etsu Na Yaba Rasuwa

  • Yanzu muke samun labarin rasuwar basaraken Abuja, Etsu na Yaba da ke yankin Abaji a birnin na tarayya
  • Allah ya yiwa Alhaji Abdullahi Adamu rasuwa ne a hanyarsa ta zuwa masallaci don yin sallar Magriba a jiya Alhamis
  • Dangin kusa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace za a yi jana'izarsa a ranar Juma'a da misalin karfe 9 na safe

Abaji, Abuja - Alhaji Abdullahi Adamu, wani fitaccen basaraken gargaji na Yaba a yankin Abaji na babban birnin tarayya Abuja ya kwanta dama.

Wani dangin basaraken, Shu’aibu Abdullahi ne ya tabbatar da hakan ga jaridar Daily Trust a ranar Alhamis.

A cewarsa, marigayi Etsu na Yaba ya rasu ne a hanyarsa ta zuwa sallar Magriba a cikin masarautar tasa.

Allah ya yiwa basaraken Abuja rasuwa
Marigayi Alhaji Abdullahi Adamu, Sarkin Yaba | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Yadda lamarin ya faru da kuma rahoton likitoci

Kara karanta wannan

Nwosu: Za a Fara Zaman Makoki a APC, Shugaba a Jam’iyya Ya Rasu a Asibiti

A cewar Shu’aibu, sarkin ya yanke Jiki ne nan take, sai fadawansa suka yi gaggawar tafiya dashi asibiti domin duba abin da ya faru.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai, an yi rashin sa’a sarkin ya yi sallama da duniya, kamar yadda majiyar ta tabbatar..

A kalamansa:

“Yana faduwa, suka dauke shi zuwa cikin mota tare da zarcewa asibiti. Amma an yi rashin sa’a ana isa asibitin, likitoci suka ce ya rasu.”

Za a yi jana'iza a ranar Juma'a

Jaridar ta tattaro cewa, an dauki gawar dattijon basaraken mai shekaru 62 zuwa masarautar Yaba domin yin jana’izarsa da misalin karfe 9 na safiyar yau Juma’a 9 ga watan Maris.

Wannan lamari dai na zuwa ne bayan rasuwar Etsu na Kwali shi ma a babban birnin tarayya Abuja, Alhaji Sha’aban Audu Nizaz, wanda ya rasu a wani asibitin kudi na Abuja a ranar 29 ga watan Disamban bara.

Kara karanta wannan

Labari Mai Zafi: Basarake Ya Kife a Cikin Fada, Ya Rasu a Hanyar Tafiya Masallaci

Allah ya yi wa ɗan Sarki a Yobe rasuwa

An shiga alhini a jihar Yobe yayin da aka samu labarin rasuwar dan Mai Martaba sarkin Gazargamu, Ibrahim Tijjani Saleh, Hakimin Laruski.

Rahoto ya bayyana cewa, basaraken ya rasu ne a sanadiyyar hadarin da auku dashi a cikin a daidaita sahu.

Mai Martaba Sakin Bade, Alhaji Abubakar Sulaiman ya mika sakon ta'aziyyarsa ga Sarkin na Gazargam, Alhaji Tijjani Saleh Geidam, inji rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel