Labari Mai Zafi: Basarake Ya Kife a Cikin Fada, Ya Rasu a Hanyar Tafiya Masallaci

Labari Mai Zafi: Basarake Ya Kife a Cikin Fada, Ya Rasu a Hanyar Tafiya Masallaci

  • Basaraken da yake mulki a Yaba, Alhaji Abdullahi Adamu ya yi mutuwar fuju’a a ranar Alhamis
  • Bayan rana ta fada ne Mai martaba Abdullahi Adamu ya fadi, zai tafi yin sallah a cikin fadarsa
  • Da aka isa babban asibiti da ke Abaji, likitoci suka tabbatar da Sarkin yayi ban-kwana da Duniya

Abuja - Wani Basarake a kasar Yaba a karamar Hukumar Abaji a babban birnin tarayya na Abuja, Alhaji Abdullahi Adamu ya rasu.

Mai martaba Abdullahi Adamu ya rasu ne a daren Juma’ar nan, labarin cikawarsa ta zo a jaridar nan ta Daily Trust a yammacin Alhamis.

Wani ‘danuwan Sarkin, Shuaibu Abdullahi ya tabbatarwa manema labarai cewa an rasa Basaraken.

Malam Shuaibu Abdullahi ya ce Etsun Yaba ya gamu da ajalinsa ne yayin da yake hanyar zuwa sallar Magriba a cikin fadarsa a jiya.

Kara karanta wannan

Hukumar INEC ta mamayi Shugaban Kasa, an daga zaben Gwamnoni bai da labari

Etsu ya yi kyakkyawan karshe

‘Danuwan Marigayin ya ce a hanyarsa ta zuwa Sallah ne ya fadi, sai fadawa suka dauke shi zuwa babban asibitin da yake garin Abaji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce a asibitin ne ma’aikatan lafiya suka tabbatar da cewa Abdullahi Adamu ya cika.

Asibiti
Wani asibiti a Abuja (Ba a nan Sarkin ya rasu ba) Hoto: www.visitandcare.com
Asali: UGC

Yana fadi, nan take suka sa shi a cikin mota, aka tafi asibiti. Amma abin takaici, da isa asibiti Likitoci suka tabbatar da ya rasu.”

- Shuaibu Abdullahi

Gobe za a birne Mai martaba

Majiya ta shaida cewa an dauke gawar Mai martaba Abdullahi Adamu daga asibitin, an wuce da shi zuwa Yaba domin ayi masa sutura.

A safiyar Juma’ar nan za ayi wa Sarkin sallah da karfe 9:00, daga nan kuma sai a birne shi.

Basarajen ya bar Duniya yana da shekaru 62, shi ne Sarki na biyu da aka rasa a birnin Abuja a cikin ‘yan watanni uku da suka wuce.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari Ya Fayyace Komai Bayan An Ga Babu Sunansa Cikin Lauyoyin Tinubu

Idan ba a manta ba, a karshen 2022 ne Etsun Kwali, Alhaji Sha’aban Audu Nizaz ya rasu a wani babban asibitin kudi da ke garin Abuja.

Emefiele yana yi wa kotu rashin kunya

An ji labari Farfesa Itse Sagay (SAN) ya ce Gwamnan babban babban bankin kasar nan zai samu kan sa da laifin sabawa hukuncin kotu.

Shugaban na PACAC ya ce duk hukuncin da kotun koli ta zartar yana aiki a kan kowa, har da Gwamnati da kuma Shugaban Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel