Manyan Jiga-Jigan PDP da Makusantan Tsohon Gwamna Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Katsina

Manyan Jiga-Jigan PDP da Makusantan Tsohon Gwamna Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Katsina

  • Jiga-jigan jam’iyyar PDP a jihar Katsina sun bayyana sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulkin jihar gabanin zaben gwamnoni
  • Jam’iyyar ta APC ta bayyana jin dadi da kuma gwarin gwiwar cin zabe a irin wannan lokacin bayan nasarar samun sabbin mambobi
  • Ana ci gaba da shirin zaben gwamnoni a Najeriya, a ranar 11 ga watan Maris ne za a yi zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi

Jihar Katsina - Jam’iyyar APC a jihar Katsina ta karbi manyan mambobin jam’iyyar PDP bakwai da magoya bayansu sama da 10,000 a ranar Talata.

Da yawan wadanda suka sauya shekan sun kasance na kusa da tsohon gwamnan jihar, Alhaji Ibrahim Shema, inji rahoton PM News.

Daraktan kamfen APC a jihar Katsina, Mr. Ahmed Musa Dangiwa ne ya bayyanawa manema labarai rahoton yadda jiga-jigan PDP na jihar suka koma APC.

Kara karanta wannan

Ba za ku iya taimakon Atiku ba: Shehu Sani ya bi kan su Wike, ya yi musu wankin babban bargo

APC ta yi sabbin mambobi daga PDP a Katsina
Jam'iyyun siyasa guda biyu da adawa da juna a Najeriya | Hoto: gazettengr.com
Asali: UGC

Gwamna ya karbi sabbin mambobin jam'iyyar APC

A cewarsa, gwamna Aminu Masari na jihar ne ya karbi wadannan jiga-jigai zuwa APC gabanin zaben gwamna da ke tafe a karshen makon nan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa:

“Daga cikinsu akwai Alhaji Bashir Tanimu Dutsinma, tsohon mai taimakawa gwamna Shehu, tsohon shugaban karamar hukuma da kuma mamban kwamitin amintattu na zauren Arewa maso Yamma a PDP.”

Ya kara da cewa, sauran jiga-jigan siyasar sun hada da shugabanni da manyan ‘yan kasuwan jihar Katsina, rahoton People's Gazette.

Musa Dangiwa ya kuma bayyana cewa, sauya shekar jiga-jigan na PDP zuwa APC alama ce ta nasara ga zaben gwamna da na ‘yan majalisun jiha a ranar 11 ga watan Maris.

Dan takarar gwamna a jam’iyyar Labour ya janye daga takara a Adamawa

A wani labarin kuma, jam’iyyar APC a jihar Adamawa ta samu karuwa yayin da dan takarar jam’iyyar Labour na gwamna ya sauya sheka, inji rahotanii daga jihar.

Kara karanta wannan

2023: Gwamna Wike Ya Ƙara Rikita Lissafin APC Ana Dab da Zaben Gwamnoni a Najeriya

Umar Otumba ya ce, ya janye daga takarar gwamna tare da marawa Aisha Ahmed Binani baya a zaben 11 ga watan Maris.

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da jam’iyyar ta APC a Adamawa ke bayyana kaunarta ga kafa gwamnati a zaben nan mai zuwa nan da kwanaki uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel