Wike Ya Fadi Abinda Yake Yi Yayin da Atiku da Jigan-Jigan Ke Zanga-Zanga

Wike Ya Fadi Abinda Yake Yi Yayin da Atiku da Jigan-Jigan Ke Zanga-Zanga

  • Gwamnan Ribas ya yi shaguɓe ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abhbakar, da sauran jiga-jigan PDP
  • Ya ce a lokacin da suka tsunduma zanga-zanga ka'in da na'in shi kuma yana zuba wa talakawansa aiki
  • A yau Litinin, Atiku ya jagorancin gwamnoni da manyan kusoshin PDP zuwa hedkwatar INEC

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya taɓo tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, wanda ya jagoranci shugabannin PDP suka yi zanga-zanga a Ofishin INEC.

Wike ya yi wa Atiku da 'yan tawagarsa shaguɓe bayan sun gudanar da tattaki zuwa Hedkwatar INEC da ke Abuja domin nuna rashin aminta da sakamakon zaɓen 25 ga watan Fabrairu.

Gwamna Wike da Atiku.
Gwamna Wike ya tsokani Atiku Hoto: channelstv
Asali: UGC

Gwamnan ya yi tsokaci kan batun ne yayin kaddamar da titin Chokocho-Igbodo, da ke ƙaramar hukumar Etche ta jihar Ribas, kamar yadda Channels ta rahoto.

Kara karanta wannan

"Bamu Haɗa Baki da Kowa Ba" INEC Ta Saurari Su Atiku, Ta Faɗi Matakin da Zata Dauka Kan Zaben Shugaban Kasa

Ya ce tun da wuri ya gargaɗi shugabannin PDP amma suka ƙeƙashe kasa suka dage sai arewa ta rike tikitin shugaban ƙasa da kujerar shugaban jam'iyya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike ya ce:

"Yayin da wasu suke zanga-zangar nuna fushi, ni ina nan ina kaddamar da ayyuka ba ruwana da wata zanga-zanga, burina na zuba ayyukan da zasu sa mutane farin ciki."

Bayan haka Wike ya yaba wa mazauna jihar bisa zaɓar shugaban ƙasa dan kudancin Najeriya a zaben da aka kammala kwanan nan.

A cewarsa, sashi na 7(3)(c) na kundin mulkin PDP ya tanadi tsarin karba-karba a kujerar shugaban kasa amma jagororin jam'iyya suka take wannan sashi.

Daily Trust ta rahoton gwamnan ya ci gaba da cewa:

"Ba wanda ke bina bashin neman afuwa, ina cikin waɗanda suka tsaya kai da fata mulki ya koma kudu saboda adalci da daidaito."

Kara karanta wannan

Hotuna: Tashin hankali ga APC, yayin da Atiku ya jagoranci PDP a zanga-zangar kin sakamakon zabe

"Idan LP ka zaɓa ban da matsala, haka idan ka zaɓi APC ka mun daidai domin abinda na jima ina yaƙi a kai kenan, tun da arewa ta yi shekara 8, ya zama wajibi kudu ta karɓa."

Yan sanda na neman ɗan takarar gwamna ruwa a jallo

A wani labarin kuma Yan Sanda Sun Ayyana Neman Dan Takarar Gwamnan APGA Kan Kisan Basarake

Rundunar yan sandan jihar Ebonyi ta nemi taimakon mutane a kokarin damƙe ɗan takarar gwamna a inuwar APGA da wasu mutane 9.

Kakakin yan sanda ya ce suna zargin mutane 10 da haɗa baki a kisan wani Basarake makon da ya gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel