Hotunan Yadda Atiku, Ayu da Tambuwal Suka Jagoranci Zanga-Zangar a Ofishin INEC

Hotunan Yadda Atiku, Ayu da Tambuwal Suka Jagoranci Zanga-Zangar a Ofishin INEC

  • Jam’iyyar PDP ta fito domin nuna adawa da yadda ta sha kaye a zaben shugaban kasa da aka yi kwanan nan
  • Dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar da sauran jiga-jigan PDP ne suka bayyana a helkwatar INEC
  • A tun farko, Bola Tinubu na APC ne ya ci zabe a Najeriya, amma PDP ta ce sam bata amince da sakamakon zaben ba

FCT, Abuja - Hotuna sun yadu a kafar sada zumunta na yadda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya jagoranci zanga-zangar nuna kin amincewa da sakamakon zaben shugaban nasa na 2023.

Atiku Abubakar na tare da sauran jiga-jigan PDP, ciki har da shugaban jam’iyyar na kasa, Ayu Iyorchia da gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal a helkwatan INEC da Abuja.

Sauran wadanda ke cikin zanga-zangar sun hada da; shugaban kwamitin kamfen na PDP, kuma gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanuel da dai sauran manyan masu fada a ji a jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 9 da Jiga-Jigan Jam’iyyar PDP Za Su Taso INEC a Gaba a Kan Nasarar Tinubu

Su Atiku sun yi zanga-zanga a Abuja
Hotunan lokacin da su Atiku suke zanga-zanga | Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

A tun farko, dan takarar na PDP ya ce bai amince da sakamakon zaben shugaban kasan da ya kawo Bola Ahmad Tinubu a matsayin wanda ya lashe zabe ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

PDP da dan takarar sun zargi almundahana da siyan kuri’u a lokacin zaben na shugaban kasa da aka gudanar, rahoton Channels Tv.

Zanga-zanga ta barke a Abuja

Wannan ne yasa suka shirya gagarumin zanga-zanga don nuna fushinsu da kuma neman a soke zaben da aka gudanar a karshen makon jiya.

A hotunan da muka gani, an ga lokacin da jiga-jigan PDP da mabiya jam’iyyar a cikin motoci sanye da bakaken kaya suna karade titunan da ke zagaye da helkwatar INEC.

Kalli hotunan, kamar yadda The Nation ta yada:

Kotu ya ce Atiku da Obi za su iya duba kayan aikin INEC

Kara karanta wannan

Zaben Jihohi: Gwamnoni da ‘Yan Takara 11 da Ke Cikin Dar-Dar Bayan Zaben Shugaban Kasa

A wani labarin kuma, kun ji yadda kotun koli ya ba ‘yan takarar shugaban kasa a LP da PDP damar duba kayan aikin zabe.

Wannan na zuwa ne bayan da suka bayyana rashin amincewa da sakamakon da aka fitar a kwanakin baya.

Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da kai ruwa rana kan sakamakon zaben da ya kawo Tinubu a matsayin shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel