Bamu haɗa baki da wata jam'iyya ba, INEC ta maida martani ga su Atiku

Bamu haɗa baki da wata jam'iyya ba, INEC ta maida martani ga su Atiku

  • INEC ta saurari Atiku Abubakar da sauran shugabannin PDP da suka gudanar da zanga-zanga a Abuja
  • Kwamishinan yaɗa labarai na INEC, Festus Okoye, ya karbi takardar da ke kunshe da korafe-korafen PDP
  • Shugaban PDP na ƙasa, Mista Ayu, ya ce wajibi INEC ta soke zaben shugaban ƙasa ta shirya sabo

Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ce zata duba "Damuwar" jam'iyyar PDP game da zaben shugaban ƙasan da aka kammala ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu.

Festus Okoye, kwamishinan yaɗa labarai na INEC, ne ya yi wannan furucin yayin da yake jawabi ga mambobin PDP da suka fito zanga-zanga a hedkwatar hukumar da ke Abuja.

Zanga-zangar PDP a Abuja.
Yadda mambobin PDP suka yi zanga-zanga a Abuja Hoto: @thecable
Asali: Twitter

Okoye ya ce takardar zanga-zangar da suka gabatar, zai damƙa wa shugaban INEC hannu da hannu kuma za'a duba damuwar da suka hango.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Wahala Ta Ƙare, Wasu Bankuna Sun Fara Baiwa Mutane Tsoffin N500 da N1000

"Na karbi takardar ƙorafin ku a madadin shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu kuma na muku alkawarin zata kai kan teburinsa," inji Okoye.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

The Cable ta rahoto Okoye na cewa:

"Idan akwai wasu ƙananan batutuwa da kuke son a ɗau mataki, zamu magance su amma ina mai kara tabbatar muku hukumar zaɓe na da kunnen sauraron koken 'yan kasa."
"Wannan hukumar ta kowa ce kuma ta 'yan Najeriya ce, INEC ba ta kulla kawance da kowace jam'iyya ba. Bamu haɗa baki da kowace jam'iyya ko ɗan takara ba."
"Ƙawancen da muka kulla da ɗaukacin al'umman tarayyan Najeriya ne, ina ƙara gode muku bisa yadda kuka yi zanga-zanga cikin lumana."

A rahoton Premium Times, Okoye ya kara da cewa INEC ta 'yan Najeriya ce kuma ba ta da alaƙa da kowace jam'iyya kuma duk wani ƙorafi zata zauna ta yi nazari a kai kana ta magance su.

Kara karanta wannan

Hotuna: Tashin hankali ga APC, yayin da Atiku ya jagoranci PDP a zanga-zangar kin sakamakon zabe

Muna son a canja sabon zabe - Ayu

Da yake gabatar da takardar korafin, shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu, ya ce ya zama dole INEC ta soke zaben shugaban kasa kuma ta canja sabo, "Wanda yan Najeriya zasu aminta da shi."

Bankuna Sun Ci Gaba da Baiwa Mutane Takardun N500 da N1000

A wani gefen kuma, kwanaki kaɗan bayan Kotun koli ta yanke hukunci kan sauya fasalin naira, Bankuna sun fara baiwa mutane tsoffin naira

A wani kwarya-kwaryan bincike da aka gudanar, akalla bankunan kasuwanci uku ne suka fara biyan kwastomominsu da tsohon N500 da N1000 a Abuja.

Haka zalika bayanai sun nuna akwai wani banki gusa ɗaya da ya fara cika umarnin Kotun koli a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel