Bola Tinubu Ya Kafa Kwamitin Sulhu Don Ganawa da Peter Obi da Atiku Abubakar, Inji Akeredolu

Bola Tinubu Ya Kafa Kwamitin Sulhu Don Ganawa da Peter Obi da Atiku Abubakar, Inji Akeredolu

  • Gwamnan jihar Ondo ya bayyana shirin Bola Ahmad Tinubu kan sauran ‘yan takarar da ya buga da kasa a zaben bana
  • Gwamnan ya ce, Tinubu ya kafa kwamitoci domin ganawa da su Atiku da Obi don dinke barakar da ka iya tasowa a gaba
  • An yi zabe a Najeriya, Tinubu ya fi dukkan ‘yan takarar tara yawan kuri’u, wasu ‘yan takara sun bayyana rashin amincewar

FCT, Abuja - Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya bayyana cewa, zababben shugaban kasan Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya kafa wani kwamitin sulhu bayan lashe zaben 2023.

Gwamnan ya ce, kwamitin zai zauna ne da sauran ‘yan takarar da suka fafata da Tinubu a zaben ranar 25 ga watan Faburairu domin yin sulhu da su.

A cewarsa, kwamitin zai hada da manya kuma dattawan jam’iyyar APC mai mulki, kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Atiku da Peter Obi Sun Ki Sallamawa Bola Tinubu, Sun Fadi Matsayar da Za Su Dauka

Bola Ahmad Tinubu zai gana da su Atiku nan ba da jimawa ba
Bola Ahmad Tinubu, zababben shugaban kasa a Najeriya | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Gwamna Rotimi ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja a lokacin da INEC ta ba Tinubu takardan shaidan lashe zaben bana.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda zaben bana ya kasance

A zaben na bana, Tinubu ne ya samu yawan kuri’un da 8,794,726, Atiku ya samu 6,984,520 sai kuma Peter Obi mai kuri’u 6,101,533.

A wata sanarwar da Richard Olatunde, sakataren yada labarai na gwamna Rotimi ya fitar, ya ce wannan zaben ya yi daidai da muradin masu kada kuri’u, Daily Post ta ruwaito.

Sannan, gwamnan ya ce duk wani dan takarar da bai ji dadin sakamakon ba, za a zauna dashi domin yin sulhu.

A kalamansa:

“Zababben shugaban kasan ya kafa kwamitoci don ganawa da ‘yan takarar da suka fafata a zaben domin a fara duba hanyar warkar da lamura.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: El-Rufai ya taya Tinubu murnar lashe zabe, ya fadi abin da Tinubu zai yiwa kasa

“Ni ina cikin daya daga cikin kwamitocin. Za mu gana dasu kuma mu roke su da su yi aiki tare da mu.

An ba Tinubu shaidar shi ya lashe zaben bana

A tun farko kunji cewa, hukumar zabe ta INEC ta kira Bola Tinubu da abokin takararsa, Kashim Shettima domin ba su shaidar lashe zabe a bana.

Wannan na zuwa ne jim kadan bayan da Farfesa Mahmud Yakubu ya ayyana Tinubun a matsayin wanda ya lashen shugaban kasa a Najeriya.

Bayan taron, Tinubu ya yi maganganu masu daukar hankali game da shirinsa ga kasa Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel