Shehi Zai Zama ‘Dan Majalisa a NNPP, Ya Canji Mahaifinsa da ya Rasu a Makon Zabe

Shehi Zai Zama ‘Dan Majalisa a NNPP, Ya Canji Mahaifinsa da ya Rasu a Makon Zabe

  • Abdulhakeem Kamilu Ado Wudil ya samu kujerar Wudil da Garko a Majalisar Tarayya a Kano
  • A sanadiyyar rasuwar Hon. Kamilu Ado Wudil, ‘dan sa ne ya shiga takarar kujerarsa a NNPP
  • Sheikh yana da cibiyar koyar da addini a Masallacin Jami’ar KUST Wudil da wasu Majalisai a jihar

Kano - Abdulhakeem Kamilu Ado Wudil ya yi nasara a zaben ‘dan takaran majalisar wakilan tarayya na shiyyar Wudil da Garko a zaben 2023.

Legit.ng Hausa ta fahimci Malam Abdulhakeem Kamilu Ado Wudil na jam’iyyar adawa ta NNPP ne ya lashe zaben majalisa da aka yi a jiya.

Matashin ya maye gurbin mahaifinsa, ACG Kamilu Ado Wudil wanda ya rasu ana shirin zabe.

Kamar yadda Ibrahim Adam ya sanar a shafinsa na Facebook, Abdulhakeem Kamilu Ado Wudil ya samu takara a NNPP ne saboda nagartarsa.

Kara karanta wannan

Kwankwaso Ya Tashi da Kuri’a 1 Kacal Yayin da Atiku Ya Kawowa PDP Akwatinsa

Ga ilmin Kur'ani, ga Hadisi

Adam wanda daya daga cikin ‘yan kwamitin takarar NNPP ne ya bayyana cewa ‘dan majalisan tarayyan mai jiran rantsarwa mahaddacin Kur’ani ne.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bugu da kari, wannan Bawan Allah makarancin Hadisin Manzon Allah (SAW) da fikihun musulunci ne, sannan ya yi karatun zamani na Boko.

Abdulhakeem Kamilu Ado Wudil
Sheikh Abdulhakeem Kamilu Ado Wudil Hoto: @Ibraheemz01 da @KwankwasoRM
Asali: Facebook

Abdulhakeem Kamilu Wudil ya san Boko

Sabon shiga siyasar ya yi digirinsa a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, kuma yanzu yana yin digirgir a bangaren kiwon lafiya na MPH a jami’ar.

Baya ga digirinsa, ‘dan majalisar mai jiran gado ya yi karatu CCNA da Difloma daga jami’ar kimiyya da fasaha da ke Wudil da wasu makarantun.

Abdulhakeem Wudil ya na karantarwa a jami’ar nan ta Al-Istiqama ta garin Sumaila.

Legit.ng Hausa ta fahimci Sheikh Wudil shi ne Darektan cibiyar Al-Auza’i da ke nazari da binciken a kan harkar addinin Musulunci a Najeriya.

Kara karanta wannan

Ana Gobe Zabe: Jam'iyyar APC ta Dakatar da Babban Yayan Gwamna Sani Bello

"Mutumin kwarai ne"

Malamin musuluncin nan, Sheikh Kabir Asgar ya shaida mana Abdulhakeem Kamilu Wudil abokinsa ne, kuma ya yi masa shaidar kirki.

Kabir Asgar ya ce Marigayi Kamilu Ado ya yi aiki da Rabiu Kwankwaso, bayan rai ya yi halinsa, sai aka zakulo shi domin ya karbi takarar Marigayin.

Malam Ibrahim El-Caleel ya ce:

"Barka da nasara, Hon (Sheikh) Abdulhakeem Kamilu Ado.
Allah Ya maka jagoranci. Allah Ya ji kan Hon., Amin. Mu na murna!”

Rasuwar ACG Wudil

A makon da ya gabata, rahoto ya zo cewa Jam’iyyar NNPP ta rasa Kamilu Ado Wudil wanda yake cikin ‘yan takaran majalisa a Kano a zaben 2023

Ana saura kasa da mako daya a shirya zaben majalisar wakilan tarayya, Hon. Wudil ya rasu, jami'in tsaron ya yi aiki da Rabiu Kwankwaso a Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel