Allahu Akbar: Saura Kwanaki 6 Zabe, ‘Dan Takaran Jam’iyyar NNPP Ya Rasu a Kano

Allahu Akbar: Saura Kwanaki 6 Zabe, ‘Dan Takaran Jam’iyyar NNPP Ya Rasu a Kano

  • Jam’iyyar adawa ta NNPP ta rasa Kamilu Ado Wudil wanda yake cikin ‘yan takaran zaben 2023
  • Majiyoyi da-dama sun tabbatar da rasuwar ‘dan takaran ana saura kasa da mako daya a shirya zabe
  • Hon. Kamilu Ado Wudil shi ne yake harin kujerar ‘dan majalisar tarayya na Wudil/Garko a NNPP

Kano - Rahotanni sun tabbatar da rasuwar Kamilu Ado Wudil wanda yake neman zama ‘dan majalisar tarayya a zabe mai zuwan nan.

Leadership ta ce Hon. Kamilu Ado Wudil mai neman kujerar ‘dan majalisar wakilan tarayya na mazabar Wudil da Garko ya bar Duniya.

‘Dan siyasar ya rasu ne a Kano a lokacin da ake shirye-shiryen zaben shugaban kasa da kuma ‘yan majalisar tarayya a duk jihohin Najeriya.

Kamilu Wudil ne yake rike da tutar jam’iyyar NNPP a takarar ‘dan majalisar Wudil da Garko, yana harin lashe zabe a makon nan da aka shiga.

Kara karanta wannan

Kuna cutar da talakawa: Atiku ya caccaki CBN da Buhari kan sabuwar dokar kudi

Zabe ya zo, ajali ya yi kira

Mutuwar ta zo ne a lokacin da kwanaki shida suka rage hukumar INEC ta gudanar da babban zabe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahoton ya bayyana cewa Marigayin ya rike shugaban karamar hukumar Wudil a lokacin da Rabiu Musa Kwankwaso yana Gwamna a 1999.

NNPP.
Hon. Kamilu Isa Wudil Hoto: politicsdigest.ng
Asali: UGC

Hon. Wudil ya yi shekaru uku a matsayin shugaban karamar hukumarsa har zuwa shekarar 2002.

Darektan kafofin sadarwa na zamani na kwamitin yakin zaben NNPP a jihar Kano, Salisu Yahaya Hotoro ya yi maganar wannan rasuwa a jiya.

A game da mutuwar jami'in na NSCDC, a Facebook aka ji Malam Hotoro yana cewa:

"Rai bakon Duniya, Allah ka gafartawa ACG Kamilu Ado Isah.:

Abdullahi Ibrahim daya daga cikin masu tallata siyasar Kwankwasiyya a dandalin sada zumunta ya tabbatar da wannan labari mai ban takaici.

Kara karanta wannan

Jerin Malaman Addini 5 da Suka Shiga Siyasa, Suke Neman Takara a Zaben 2023

Malam Abdullahi Ibrahim ya rubuta a shafin Twitter:

"Allah ya masa Innalillahi Wa'innah Ilaihir Raji'un. ‘Dan takaran NNPP na majalisar wakilan tarayyar Wudil/Garko, Hon Kamilu Ado Isah, ya rasu.

Allah ya masa rahama Ameen."

DSS ta cafke FFK a Abuja

Femi Fani-Kayode wanda aka fi sani da FFK ya ce ya ji babu dadi a lokacin da ya shiga ragar DSS a sakamakon bayanan da ya rika yi da bakinsa.

Jagoran na APC ya ce ya shafe tsawon kusan sa’o’i biyar hannun DSS, an taso shi a gaba da matsa; ana bincikensa ni da kyau kan zargin juyin mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel