Kwankwaso Ya Tashi da Kuri’a 1 Kacal Yayin da Atiku Ya Kawowa PDP Akwatinsa

Kwankwaso Ya Tashi da Kuri’a 1 Kacal Yayin da Atiku Ya Kawowa PDP Akwatinsa

  • ‘Dan takaran Shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar ya yi zarra a rumfarsa
  • A akwatin yankin Jada inda Wazirin Adamawa yake zabe, ba a maganar kowa sai jam’iyyar PDP
  • Bola Tinubu ya samu kuri’a 57, sai Peter Obi da Rabiu Kwankwaso suka zo na uku da na hudu

Adamawa - Atiku Abubakar mai neman takarar shugabancin Najeriya a karkashin babbar jam’iyyar PDP ya samu galaba a akwatin zabensa.

Jami’in zaben hukumar INEC na rumfar zaben da ke garin Jada, Nalawu Phillip ya tabbatar da cewa Atiku Abubakar ya samu kuri’u 282 a zaben.

Daily Trust ta ce wanda ya zo na biyu shi ne ‘dan takaran jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu. APC da Asiwaju Bola Tinubu sun samu kuri’u 57.

Yayin da Peter Obi ya zo na uku da kuri’u shida a zaben, Rabiu Musa Kwankwaso mai neman mulki a jam’iyyar adawa ta NNPP ya kare da daya.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Sakamakon Zaben Akwatin Atiku Ya Fito, Ya Lallasa Tinubu da Kwankwaso

A halin yanzu dai ana cigaba da tattara kuri’un zaben shugaban kasar ne daga jihohin kasar nan.

Atiku
Atiku yana kada kuri'a a Jada Hoto: @Atiku.org
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da Wazirin Adamawa ya kawo akwatinsa, shi ma Bola Tinubu ya yi nasara a inda Muhammadu Buhari da Yemi Osinbajo suke zabe.

A Ikenne inda mataimakin shugaban kasa yake zabe, jam’iyyar APC ta samu kuri’u 33, Peter Obi da Atiku Abubakar sun tsira da tara da bakwai.

Obi ya kawo rumfarsa

A inda Peter Obi ya yi zabe a mazabar Agulu a karamar hukumar Anaocha, APC da PDP ba su samu ko kuri’a guda a zaben shugaban kasa ba.

Jam’iyyar LP ta yi nasara da kuri’u 236, APGA mai rike da kujerar Gwamna a jihar ta lashe kuri’u uku, sai Rabiu Kwankwaso ya ci kuri’u biyu.

The Cable ta ce sauran jam'iyyu ba su iya kai labari a akwatin tsohon Gwamnan ba.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bayan Shugaban PDP, An Sake Samun Wani Shugaban Jam'iyya Ya Mutu a Abuja

NNPP za ta kai labari?

A game da zaben bana, mun zanta da Saifullahi Hassan, wanda Hadimin Rabiu Musa Kwankwaso mai neman zama shugaban kasa a NNPP.

Saifullahi Hassan ya tabbatar mana da cewa su na hangen nasara a kujerun da aka fafata, ya ce su na masu sa ran lashe zaben 100 bisa 100.

"Ai yadda al'umma suka fito suka yi zabe, babu maganar wani magudi, saboda duk inda ka je, za ka ga sai (ratar NNPP) ta nunka sau nawa.
To babu maganar wani magudi, kuma a wajen za ka ga sakamakon zaben ana tura shi yana tafiya, kuma kowa ya sani, idan Allah ya yarda babu matsala..."

- Saifullahi Hassan

Asali: Legit.ng

Online view pixel