Zaben 2023: Tinubu Na Gaban Obi da Atiku a Ondo Yayin da Sakamakon Zabe Ke Fitowa

Zaben 2023: Tinubu Na Gaban Obi da Atiku a Ondo Yayin da Sakamakon Zabe Ke Fitowa

  • Sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu na ci gaba da fitowa
  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na APC ne a kan gaba a sakamakon kananan hukumomi uku na jihar Ondo da ka sanar zuwa yanzu
  • Yankunan da aka sanar zuwa yanzu sun hada da Akure ta arewa, Akoko ta kudu maso gabas da kuma Akoko ta kudu maso yamma

Ondo - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, ya lashe sakamakon zabe a kananan hukumomin uku na jihar Ondo da aka sanar zuwa yanzu.

Kananan hukumomin sune Akure ta arewa, Akoko ta kudu maso gabas da kuma Akoko ta kudu maso yamma, rahoton Daily Trust.

Manyan yan takarar shugaban kasa na zaben 2023
Zaben 2023: Tinubu Na Gaban Obi da Atiku a Ondo Yayin da Sakamakon Zabe Ke Fitowa Hoto: Mr. Peter Obi, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

A Akure ta arewa Tinubu ya samu kuri'u 14,261 wajen lallasa takwarorinsa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, da Labour Party, Peter Obi wadanda suka samu 4,633 da 2,945 kowannensu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bola Tinubu Ya Lallasa Atiku da Kwankwaso, Ya Lashe Zabe a Kananan Hukumomi 10

Akoko ta kudu maso gabas, Tinubu ya samu kuri'u 10,765, Atiku 3,016 yayin da Obi ya samu 470.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A Akoko ta kudu maso yamma, Tinubu ya samu kuri'u 28,367, Atiku ya samu kuri'u 5,376 yayin da Obi ya samu 920.

Ga cikakken sakamakon zaben a kasa:

Akure ta arewa

Masu rijista – 79,272

Wadanda aka tantance – 23,917

A: 24

AA: 11

AAC: 35

ADC: 288

ADP: 54

APC: 14,261

APGA: 39

APM: 19

APP: 22

BP: 21

LP: 2,945

NNPP: 66

NRM: 14

PDP: 4,633

PRP: 08

SDP: 48

YPP: 12

ZLP: 374

Jimlar kuri'u masu inganci – 22,874

Lalatattun kuri'u – 1,024

Jimlar zaben da aka kada– 23,898

Akoko ta kudu maso gabas

Masu rijista – 40,592

Wadanda aka tantance – 14,783

A: 00

AA: 00

AAC: 07

ADC: 97

ADP: 37

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Dino Melaye Ya Kawo Wa Atiku Akwatinsa A Kogi, Duba Sakamakon

APC: 10,765

APGA: 13

APM: 03

APP: 03

BP: 00

LP: 470

NNPP: 07

NRM: 08

PDP: 3,016

PRP: 05

SDP: 101

YPP: 01

ZLP: 16

Jimlar kuri'u masu inganci – 14,549

Lalatattun kuri'u – 234

Jimlar zaben da aka kada – 14,783

Akoko ta kudu maso yamma

Masu rijista — 107,651

Wadanda aka tantance – 36,383

A — 20

AA — 13

AAC — 26

ADC — 427

ADP — 91

APC — 28,367

APGA —37

APM — 10

APP — 16

BP — 7

LP — 920

NNPP — 28

NRM — 9

PDP — 5,376

PRP — 15

SDP — 161

YPP — 9

ZLP — 45

Jimlar kuri'u masu inganci — 35,577

Lalatattun kuri'u – 781

Jimlar zaben da aka kada– 36,358

A wani labari na daban, mun ji cewa wasu bata gari sun harbi mata biyu yayin gudanart da zaben shugaban kasa a jihar Bayelsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel