Tashin Hankali Ga APC Yayin da Tsohon Dan Takarar Gwamna Ya Bi Sahun Su Atiku a Jihar Sokoto

Tashin Hankali Ga APC Yayin da Tsohon Dan Takarar Gwamna Ya Bi Sahun Su Atiku a Jihar Sokoto

  • Jam’iyyar APC a jihar Sokoto ta yi babban rashi yayin da ta rasa wani jigo kuma babban danta, Faruk Malami Yabo
  • Yabo ya taba tsayawa takarar gwamna a APC a jihar, inda ya rasa tikiti bayan zaben fidda gwanin da aka gudanar a jihar
  • Gwamna Aminu Tambuwa da wasu jiga-jigan PDP ne suka karbi Yabo, wanda tsohon jakadan Najeriya ne a kasar Jordan

Jihar Sokoto ¬Tsohon dan takarar gwamna a jam’iyyar APC, Faruk Malami Yabo ya bayyana ficewa daga jam’iyyar tare da kama hanyar PDP ta su gwamna mai ci a jihar, Aminu Tambuwal.

Yabo, wanda tsohon jakadan Najeriya ne a kasar Jordan ya bayyana shiga PDP ne a lokacin da tawagar kamfen din PDP ta dura karamar hukumar Yabo a jiya Laraba 4 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

2023: Shugaban PDP Na Kasa Ya Lallaba Ya Gana da Gwamna Wike? Gaskiya Ta Bayyana

Ya bayyana shigarsa PDP a matsayin dawowa gida, inda ya ce jinin PDP ne ke yawo a jikinsa, wacce ke mulkin jihar a Arewa maso Yammacin Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Dan takarar gwamnan APC ya sauya sheka zuwa PDP
Tashin Hankali Ga APC Yayin da Tsohon Dan Takarar Gwamna Ya Bi Sahun Su Atiku a Jihar Sokoto | Hoto: Faruk Umar Kankiya
Asali: Facebook

A cewarsa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Sauya shekar daidai take da mutum ya dawo gida, Ina goodiya ga kowa da ke cikin wannan tafiya kuma na yi alkawarin taimawa jam’iyyar don ta yi nasara a zabe mai zuwa a jihar.”

Gwamna Tambuwal ta tarbi Yabo

Legit.ng ta tattaro cewa, gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ne ya karbi Yabo zuwa PDP, kuma ya yaba masa da gano gaskiya.

A cewar gwamnan, shigowa Yabo PDP ya sanya ranar ta jiya a matsayin rana mai cike da tarihi ga siyasa da dimokradiyya a jihar Sokoto.

Jaridar Vanguard ta ruwaito Tambuwal na cewa:

“Dan uwa, bayyanawarka a hukunce ka dawo PDP, jam’iyyarka na ta jira kuma babban ci gaba ne a aikin da ke gabanmu.

Kara karanta wannan

Ta Faru Ta Kare: Tsohon Mai Neman Takarar Gwamna a APC Ya Koma PDP a Jihar Arewa

“Wannan na ci gaba da nuna haske ga PDP cewa za ta yi nasara a jihar Sokoto da ma Najeriya baki daya.”

Obasanjo ya fi dukkan 'yan APC alheri, inji jigon siyasa

A wani labarin kuma, kunji yadda wani jigon siyasa a jihar su Tinubu ya yiwa Buhari da dukkan 'yan APC kudin goro, yace tsohon shugaban kasa, Obasanjo ya fi su alheri.

Ya bayyana hakan ne a martaninsa ga yadda 'yan APC suka taso Obasanjo a gaba kan goyon bayan Peter Obi a zaben bana.

Kwanaki kadan suka rage a yi zabe a Najeriya, manyan kasa na ci gaba da bayyana wadanda suke goyon baya gabanin zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel