Tsohon Mai Neman Takarar Gwamnan APC, Ambasada Yabo Ya Koma PDP a Jihar Sakkwato

Tsohon Mai Neman Takarar Gwamnan APC, Ambasada Yabo Ya Koma PDP a Jihar Sakkwato

  • Tsohon jakadan Najeriya a Jordan kuma jigon jam’iyyar APC, Faruk Yabo, ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP a jihar Sakkwato
  • Yabo wanda ya nemi takarar tikitin gwamnan APC a zaben fidda gwanin jam'iyyar da aka yi a bara ya sanar da sauya shekarsa ne a ranar Laraba, 4 ga watan Janairu
  • Gwamna Aminu Tambuwal ya bayyana dawowar Yabo PDP a matsayin gagarumin nasara a garesu

Sokoto - Tsohon mai neman takarar gwamna na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben fidda gwanin 2022 da aka yi a jihar Sakkwato, Ambasada Faruk Yabo, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) gabannin zaben 2023.

Yabo, wanda ya kasance tsohon jakadan Najeriya a kasar Jordan kuma abokin tafiyar dan takarar gwamnan APC a zaben 2019, ya bayyana a gangamin yakin neman zaben PDP da ya gudana a karamar hukumar Yabo da ke jihar a ranar Laraba, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Shugaban BoT Ya Yi Magana Kan Yuwuwar Wasu Gwamnonin PDP Su Sauya Sheka Kafin Zabe

Yakin neman zaben PDP
Tsohon Mai Neman Takarar Gwamnan APC, Ambasada Yabo Ya Koma PDP a Jihar Sakkwato Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Dawowar Yabo PDP alamun nasara ne garemu, Tambuwal

Da yake jawabi a taron, Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sakkwato, ya ce sun kasance a Yabo ne don mika godiya domin komawa PDP da Yabo ya yarda ya yi ya gama wa jam'iyyar kamfen a yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Yau ya kasance daya daga cikin ranaku mafi nasara a tarihin damokradiyya a jihar Sakkwato.
"Dan uwana, ayyana dawowarka PDP a hukumance, jam'iyyarka ta dade tana tsimayin haka kuma babban ci gaba ne a aikin da ke gabanmu.
"Wannan alama ce da ke nuna PDP za ta yi nasara a jihar Sakkwato da Najeriya gaba daya."

Tambuwal, wanda shine darakta janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP ya yi godiya ga mutanen Yabo kan goyon bayan da suke ba PDP.

Kara karanta wannan

Aiki ja: Dan wani fitaccen sanatan Arewa na APC ya bar jam'iyyar, ya koma PDP

Da yake jawabi, Yabo ya ce ya koma PDP ne saboda mutunci da amincin jam'iyyar.

Ya yi godiya ga mutanen jihar gaba daya musamman ma yan karamar hukumar Yabo kan kasancewa tare da shi, ya kuma nemawa PDP gagarumin goyon baya a zabe mai zuwa.

Dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP, Malam Sa’idu Umar, ya sha alwashin daurawa daga inda Tambuwal ya tsaya idan aka zabe shi, rahoton Thisday.

Umar ya ba taron tabbacin cewa zai tafiyar da gwamnati wacce za ta dama da kowa da aiwatar da abubuwan bukata a jihar.

Tsohon mataimakin gwamnan jihar Neja ya fice daga APC

A wani labarin kuma, tsohon mataimakin gwamnan jihar Neja, Ahmed Musa Ibeto, ya fice daga jam'iyyar APC gabannin babban zaben 2023.

Ibeto ya ce ya bar jam'iyya mai mulki a kasar ne saboda rashin hadin kai a tsakanin 'ya'yanta a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel