Shugaban PDP Na Kasa Ya Lallaba Ya Gana da Wike? Gaskiya Ta Bayyana

Shugaban PDP Na Kasa Ya Lallaba Ya Gana da Wike? Gaskiya Ta Bayyana

  • Shugaban PDP na kasa ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewa ya lallaba jihar Ribas ya gana da gwamna Nyesom Wike
  • Wike tare da mambobin tawagar G5 sun kafa sharadin sauke Ayu da maye gurbin da dan kudu kafin su goyi bayan Atiku
  • A halin yanzu ana dakon jin dan takarar da tsagin Wike suka yanke marawa baya a 2023 bayan duk wata tattaunawar sulhu ta rushe

Abuja - Shugaban Peoples Democratic Party, PDP, na kasa, Dakta Iyorchia Ayu, ya musanta rade-radin ɗa ake yadawa a kafafen sada zumunta cewa ya lallaba ya gana da gwamnan Ribas, Nyesom Wike, a Patakwal.

Dakta Ayu yace babu wani zama da suka yi tsakaninsa da gwamnan a Patakwal, babban birnin jihar Ribas ko wani wuri a fadin Najeriya, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike Ya Magantu Kan Dan Takarar Shugaban Kasan Da Zai Marawa Baya a Zaben 2023

Wike tare da Ayu.
Shugaban PDP Na Kasa Ya Lallaba Ya Gana da Wike? Gaskiya Ta Bayyana Hoto: @chief_adam
Asali: Twitter

Shugaban PDP ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawunsa, Simon Imobo-Tswam, a babban birnin tarayya Abuja ranar Laraba 4 ga watan Janairu, 2023.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa a wata sanarwa da Imobo-Tswam ya fitar, ya ce jita-jitar ta faro daga hannun masu kokarin yada karerayi da fasadi tsakanin al'umma.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Imobo Tswam ya ce:

"Dakta Ayu ya bayyana gaskiyar zance cewa ko kadan bai sa kafa a Patakwal ba kuma idonsa bai yi tozali da gwamna Wike ba a baya-bayan nan. Hoton da ake yaɗa wa a kafafen sada zumunta tsoho ne."
"Saboda haka labarin da aka jingina wa Hoton karya ce tsantsa da yunkurin ta da fitina, a halin yanzu shugaban PDP na ƙasa na tare da iyalinsa suna hutun sabuwar shekara, ba abinda ke damunsa."

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Shugaban BoT Ya Yi Magana Kan Yuwuwar Wasu Gwamnonin PDP Su Sauya Sheka Kafin Zabe

"Bisa haka muna kira ga daukacin al'umma musamman 'ya'yan jam'iyyar PDP da su shure labarin kuma su maida hankali kan aikin dake gaban jam'iyya a wata mai zuwa."

Babu Gwamnan APC Da Ya Hada Kai da Jam'iyar PDP, Atiku Bagudu

A wani labarin kuma Gwamna Bagudu ya karyata rahoton da ake yadawa cewa wasu gwamnonin APC sun hada kai da yan dawa

Gwamna Atiku Bagudu, ya karyata rahoton dake yawo cewa wasu gwamnonin APC na cin amanar Tinubu, suna wa PDP aiki a boye.

Gwamnan ya fayyace gaskiya ne a wurin gangamin kamfen Kano, wanda mutane suka cika birnin Kano ba masaka tsinke.

Asali: Legit.ng

Online view pixel