Abin da Ya Faru da Atiku a Zaben 2019 Bayan Obasanjo Ya Marawa Takararsa Baya

Abin da Ya Faru da Atiku a Zaben 2019 Bayan Obasanjo Ya Marawa Takararsa Baya

  • ‘Dan takaran Cif Olusegun Obasanjo a zaben shugaban kasa da za ayi a shekarar nan shi ne Peter Obi
  • Idan aka duba tarihi, za a fahimci goyon bayan da Obasanjo ya ba Atiku Abubakar a 2019 bai cece shi ba
  • Tsohon shugaban Najeriyan bai iya kawowa Atiku da jam’iyyar PDP rumfarsa ba a Ogun, APC tayi nasara

Ogun - A ranar Lahadi, 1 ga watan Junairu 2022, tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya fito baro-baro ya nuna yana goyon bayan Mista Peter Obi.

The Cable ta ce Cif Olusegun Obasanjo ya fadawa ‘Yan Najeriya ‘dan takararsa na zaben shugaban kasa ne a wata wasikarsa da ya fitar a sabuwar shekara.

Sai dai wannan mataki da tsohon shugaban kasar ya dauka bai ba mutane da-dama mamaki ba.

Jam’iyyun APC da PDP da ‘yan takaransu watau Bola Tinubu da Atiku Abubakar, har zuwa fadar shugaban kasa sun yi ta maidawa Cif Obasanjo martani.

Kara karanta wannan

Abin da Obasanjo Ya Fada Game da Masu Neman Mulki Yayin da Ya Fito da 'Dan takara

Meya faru a zabukan 2019?

Jaridar The Cable ta bibiyi zaben shugaban kasa da aka yi a 2019, wanda Obasanjo a karon farko ya goyi bayan Atiku Abubakar, da kuma yadda ta kaya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Atiku Abubakar mai neman zama shugaban Najeriya a karkashin inuwar PDP a zaben bana, shi ne mataimakin shugaban kasa a gwamnatin Obasanjo.

Atiku da Obasanjo
Atiku Abubakar Hoto: @Atiku.org
Asali: UGC

A tsawon shekaru takwas da gwamnatin tayi daga 1999 zuwa 2007, Atiku ya rike wannan kujera, sai dai an samu rashin jituwa tsakanin shugabannin.

A zaben 2019, Cif Obasanjo ya ajiye gabarsu a gefe, ya marawa Wazirin Adamawa baya a kan Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC mai mulkin kasa.

APC ta doke PDP a akwatin Obasanjo

Idan za a tuna, wannan goyon bayan bai iya sa Atiku Abubakar ya doke Shugaba Buhari ba.

Abin mamaki a lokacin, Obasanjo bai iya kawowa Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP ko da akwatinsa ba, APC mai rike da kasar ce ta ba shi kunya a zaben.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Yi Martani Mai Zafi Ga Obasanjo Kan Nuna Goyon Baya Ga Peter Obi

Sakamakon zaben ya tabbatar da cewa jam’iyyar PDP ta sha mummunan kashi a rumfar zabe ta 22 da ke karamar hukumar Abeokuta ta Arewa a Ogun.

A yayin da aka yi tunani tasirin Obasanjo zai yi aiki a zaben, sai ga tsohon mataimakinsa ya kare da kuri’u 18 rak, Muhammadu Buhari ya tashi da 87.

An murde zabukan 2003 - 2011

An ji labari an yi wata hira da ‘danuwan shugaban Najeriyan “Essential Muhammadu Buhari”, a nan ya yi bayanin abin da ya sa Muhammadu Buhari yin kuka.

Bayan shekaru 7 a kan mulki, Malam Mamman Daura ya fadi dalilin CPC na hadewa da ACN da APGA domin a doke jam’iyyar PDP daga kan karagar mulki

Asali: Legit.ng

Online view pixel