Abin da Obasanjo Ya Fada Game da Masu Neman Mulki Yayin da Ya Fito da 'Dan takara

Abin da Obasanjo Ya Fada Game da Masu Neman Mulki Yayin da Ya Fito da 'Dan takara

  • Olusegun Obasanjo ya na ganin babu wanda ya cancanta ya zama shugaban Najeriya irin Peter Obi
  • Tsohon shugaban kasar ya ce Obi ya fi kowa dacewa, manufofi, halaye da koshin lafiyar rike Najeriya
  • Obasanjo ya yi aiki da kusan duka manyan masu neman takarar shugabancin kasa a zabe mai zuwa

Ogun - Maganar da Olusegun Obasanjo ya yi a matsayin dalilin goyon bayan Peter Obi ya zama shugaban kasar Najeriya, yana cigaba da jawo maganganu.

A ranar Lahadi, 1 ga watan Junairu 2023, jaridar Daily Trust ta rahoto abin da ke cikin wasikar da tsohon shugaban kasar ya fitar, ya na bayyana matsayarsa.

Duk da Atiku Abubakar da Bola Tinubu sun zauna da Olusegun Obasanjo a gidansa, tsohon sojan ya ki mara masu baya a yakin neman zaben da suke yi.

Kara karanta wannan

Magana Ta Kare, Tsohon Shugaban Kasa Ya Fadi Wanda Yake Goyon Baya Ya Gaji Buhari a Zaben 2023

Cif Obasanjo wanda ya hakura da abin da ya faru a baya, ya goyi bayan Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP a zaben 2019, ya koma goyon bayan LP.

Kwanaki bayan ganawarsa da Bola Tinubu, magoya bayan ‘dan takaran na APC mai mulki sun yi kokarin nuna sun samu goyon bayan tsohon shugaban.

Legit.ng Hausa ta na da labari shi ma Rabiu Kwankwaso wanda ya yi Minista a gwamnatin Obasanjo ya hadu da tsohon mai gidansa a shekarar bara.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A wasikarsa, Obasanjo ya kawo dalilin da suka sa yake tare da Obi na LP a zabe mai zuwa. Rahoton nan ya kawo maganarsa game da ragowar ‘yan takaran.

Obasanjo
Olusegun Obasanjo Hoto: Getty Images
Asali: UGC

Ana fada mana karya da gaskiya - Obasanjo

“Mun samu masu yawon yakin neman zabe su na yawo a kasar nan, su na fada mana abin da suke nufi da wadanda ba su nufi, abin da suka fahimta da wanda ba su gama fahimta ba, mai yiwuwa da mara yiwuwa, gaskiya da karya.

Kara karanta wannan

Tsagin Atiku Abubakar Ya Fadi Gaskiya Game da Babban Asirin da Wike Ya Bankado Kan Zaben 2003

Ba tare da daukar matsaya ba, sai girmama kowane mai takara tare da la’akari da Najeriya da duk mutanenta, da kuma aikin da na yi. Duka manyan ‘yan takaran su na ikirarin ni mai gidansu. Ba zan musaya wannan maganar ba.
Nayi aiki da su kai-tsaye ko a kaikaice. Na kuma iya fahimtar halaye da dabi’un da ake bikata wajen jagorantar sha’anin Najeriya cikin nasara, musamman a irin lokacin nan. Wadannan su na cikin da-damansu da ake bukata ba.

- Olusegun Obasanjo

TVCP da Emi Lokan

"Daga tattaunawa da abin da na sani, sannan kuma da zama na jagora kamar yadda mafi yawa suke ikirari, ba tare da nuna son kai, tsoro ko tsana ba, abubuwa hudu ake dubawa a wajen wanda ke neman mulki, zan kira su TVCP."

- Olusegun Obasanjo

Obasanjo ya ce dole ayi la’akari da abin da ‘dan takara ya yi a baya, manufofinsa, sai halin kirki da kuma karfin jiki da basirar da zai iya jagorantar jama’a.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Dawo da Komai Baya, Ya Fadi Gaskiyar Batun Haduwarsa da Gwamnonin PDP

Wasikar tsohon shugaban kasar ta soki taken ‘Emi Lokan’ da Tinubu ya zo da shi, yana cewa lokacinsa ya yi da za iyi mulki, ya ce tun nan an yi kuskure.

Babu waliyyi a 'Yan takaran

Kun ji labari cewa tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya kawo karshen jita-jitar da ake yi, ya ayyana goyon bayansa ga Peter Obi a zabe mai zuwa.

Obasanjo yace babu waliyyi a cikin manema shugaban kasa amma idan aka ɗora su a sikelin ilimi da gogewa, Peter Obi ba tsaran abokan hamayyarsa ba ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel