Aikin Banza Kayi: Tinubu Ya Caccaki Obasanjo Kan Nuna Goyon Baya Ga Peter Obi

Aikin Banza Kayi: Tinubu Ya Caccaki Obasanjo Kan Nuna Goyon Baya Ga Peter Obi

  • Jam'iyyar APC ta yi tsokaci kan jawabin tsohon shugaban kasan Najeriya, Olusegun Obasanjo
  • Jam'iyyar ta APC kwanakin baya ta kai ziyara wa Obasanjo domin neman goyon bayansa
  • Dare daya Obasanjo ya yi kira ga yan Najeriya musamman matasa su zabi Peter Obi a zaben 2023

Abuja - Wakilin jam'iyyar All Progressives Congress, APC a zaben shugaban kasa da zai gudana a 2023, Asiwaju Bola Tinubu, ya yi tsokaci game da labarin sabon goyon bayan da Peter Obi na jam'iyyar Labour Party, ya samu.

Legit ta kawo muku labarin cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana goyon bayan sa ga Peter Obi a yau Lahadi, 1 ga watan Junairu, 2023.

Tinubu a martanin ya bayyana cewa wannan aikin banza ne Obasanjo yayi kuma babu wani tasirin da hakan zai yi, rahoton Vanguard.

Obasanjo
Aikin Banza Kayi: Tinubu Ya Caccaki Obasanjo Kan Nuna Goyon Baya Ga Peter Obi
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A raddin da Tinubu yayi, ya ce babu komai, Obasanjo na da huruminsa na demokradiyya ta zabi duk wanda yake so.

Tinubu ya ce tarihi ya nuna cewa wadanda Obasanjo ya marawa baya a zabukan shekarun baya duk kashi suka sha.

Ya ce ko kujerar Kansilan unguwarsa ba zai iya kawowa ba.

Obasanjo Na Tare da Gwamnonin G-5

Wata majiya mai karfi ta bayyana cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, tuni ya yi kira ga Gwamnonin G-5 su marawa Peter Obi baya.

A cewar majiyar:

"Gwamnonin na tunanin bin shawaran Obasanjo ne cewa dan kudu ne ya kamata ya zama shugaban kasa a 2023. Obasanjo ya basu shawaran su marawa Obi baya saboda yana ganin koda mulki zai koma kudu, yankin Kudu maso gabas suka yi cancanta."
"Wannan shine dalilin da ya sa a zamansu na karshe a Landan, ya ce zaben Obi shine adalci."

Majiyar ta kara da cewa lallai maganar Wike na cewa a Junairu zasu bayyana matsayarsu gaskiya ne, yace:

"Gwamnonin zasu sanar da dan takaran da zasu yi mako mai zuwa. Idan babu wani babban taro gabanin 5 ga Junairu lokacin da zai kaddamar da kamfensa, zasu sanar a ranar a Ibadan."

Gwamnonin sun hada da gwamnon Nyesom Wike na jihar Rivers, Seyi Makinde na jihar Oyo, Okezie Ikpeazu na Abia), Samuel Ortom na Benue, da kuma Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel