Zaben 2023: Tsohon Shugaban PDP da Sakataren Kudi Sun Koma NNPP a Gombe
- Damar da Atiku ke da shi na lashe zaben 2023 a jihar Gombe na fuskantar gagarumin barazana yayin da manyan mambobin PDP ke ficewa daga jam'iyyar
- Tsohon shugaban PDP a karamar hukumar Funkaya, Mohammed Kari Bajoga da sakataren kudi na jam'iyyar a karamar hukumar Dukku, Bakari Umaru Bawa, suka fice daga jam'iyyar
- Jiga-jigan biyu sun koma jam'iyyar NNPP a jihar kuma Umaru ne mai rike da mukamin PDP na biyu da ke komawa jam'iyyarsu Kwankwaso a karamar hukumar Dukku
Gombe - Damar da Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ke da shi a zaben 2023 na ci gaba da fuskantar barazana daga bangarori daban-daban na kasar.
Cikas da Atiu ya hadu da shi a baya-bayan nan shine na ficewar wasu manyan jiga-jigan PDP biyu inda suka koma jam'iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) a kananan hukumomin Funkaye da Dukku da ke jihar Gombe, Daily Independent ta rahoto.
Dalilin da yasa jiga-jigan PDP suka koma NNPP a Gombe
Mohammed Kari Bajoga, tsohon shugaban PDP a karamar hukumar Funkaya da Bakari Umaru Bawa, tsohon sakataren kudi na jam'iyyar a karamar hukumar Dukku, sun koma NNPP tare da daruruwan magoya bayansu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kari Bajoga ya samu tarba daga shugaban NNPP a karamar hukumar, Bello Mamuda, wanda ya kuma gabatar masa da katin shaidar zama dan NNPP.
Tsohon jigon na PDP ya ce ya koma NNPP ne saboda jam'iyyar ce za ta yi nasara a zaben 2023, yana mai cewa daga APC har PDP sun rasa alkiblarsu.
A daya bangaren, dan takarar gwamnan NNPP a jihar Gombe, Khamisu Ahmed Mailantarki, ya tarbi Bakari Umari a gidansa, rahoton Daylight Reporters.
Har zuwa lokacin da ya koma NNPP, Umaru shine sakataren kudi na PDP a karamar hukumar Dukku ta jihar kuma shine jami'in PDP na biyu da ya koma NNPP a yankin.
NNPP na daya daga cikin manyan jam'iyyun siyasa a zaben 2023. Dan takararta na shugaban kasa, Rabiu Kwankwaso, ya kasance tsohon minista kuma tsohon gwamnan jihar Kano.
A wani labarin kuma, mun ji cewa surukin ministan harkokin ‘yan sanda, Muhammad Maigari Dingyadi wato Zayyanu Wamakko, ya fice daga jam’iyyar APC zuwa ta PDP.
Asali: Legit.ng