Darakta Janar Na Kamfen PDP Da Wasu Jiga-Jigai Sun koma APC a Katsina

Darakta Janar Na Kamfen PDP Da Wasu Jiga-Jigai Sun koma APC a Katsina

  • Jam'iyar PDP ta sake shiga matsala yayin da dubbannin 'ya'yanta suka tattara suka koma APC a jihar Katsina
  • Har yau an gaza nemo bakin zaren rigingimun PDP a Katsina babu batun fara kamfen dan takarar gwamna, Yakubu Lado
  • Jirgin yakin Dikko/Radda ya gudanar da ralin kamfe a karamar hukumar Danmusa ranar Asabar

Katsina - Darakta Janar na kwamitin kamfen dan takarar Gwamnan Katsina karkashin PDP a zaben 2019 da ya shude, Alhaji Sani Abu, tare da wasu jiga-jigai da mambobi 1,907 sun sauya sheka zuwa PDP.

Tsohon DG na Kamfen Yakubu Lado da sauran yan siyasan sun shiga APC a hukumance ne yayin da jirgin kamfen Dikko/Jobe ya dira karamar hukumar Danmusa domin yakin neman zabe.

Taron APC a Danmusa.
Darakta Janar Na Kamfen PDP Da Wasu Jiga-Jigai Sun koma APC a Katsina Hoto: Gwagware Social Media
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa dan takarar gwamna a inuwar APC, Dikko Radda ne ya karbe su a wurin gangamin yakin neman zaben da ya gudana ranar Asabar.

Kara karanta wannan

2023: Gaskiya Ta Fito, Gwamnan APC Ya Magantu Kan Rahoton Yana Yi Wa PDP Aiki

Alhaji Abdulhamid Aliyu Danmusa, na daya daga fitattun mutane 1,907 da suka yi ayari zuwa APC, ya kasancen tsohon jami'in hukumar DSS kuma tsohon shugaban tsaro na bankin arewa da aka rushe.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An ce manyan mutanen biyu, tsohon DG Sani Abu Minista da Abdulhamid Aliyu suna karfin faɗa a ji a yankin karamar hukumar Danmusa da ke Katsina.

Bugu da kari, Minista ya ba da kyautar Ofishin kamfe wanda Dakta Dikko Radda ya kaddamar yayin ralin kamfen.

Meyasa suka sauya sheka zuwa APC?

Daya daga cikin jiga-jigan masu sauya shekar kuma tsohon dan takarar majalisar wakilan tarayya, Honorabul Lawal Shuaibu, yace sun shiga APC ne saboda suna kaunar ci gaban al'umma.

Ya ce:

"Mun koma APC ne saboda muna son mutane su samu ci gaba, rigimgimu sun yi wa PDP katutu ga shi zabe ya karato nan da watanni biyu. Ta ya suke tunanin cin zabe bayan an tsige shugaba."

Kara karanta wannan

Tsagin Atiku Abubakar Ya Fadi Gaskiya Game da Babban Asirin da Wike Ya Bankado Kan Zaben 2003

"Mun ba al'umma tabbacin yin wani abu amma ranar zabe na kara karatowa har yanzu jam'iyar ba ta fara kamfe ba yayin da tuni APC ta gama shiyya guda, yanzu gamu a shiyya ta biyu."

Karamar hukumar Danmusa nan ne mahaifar tsohon Sakataren gwamnatin Katsina, Mustapha Inuwa, wanda ya koma PDP kuma ya zama Daraktan Kamfen Atiku-Lado 2023.

Yan daba sun farmaki Ayarin Tambuwal

A wani labarin kuma Tsageru Sun Kaiwa Ayarin Gwamnan Sakkwato Na Hannun Daman Atiku Hari, Sun Tafka Barna

Wasu mutane da ba'a san su waye ba sun yi wa Ayarin gwamna Aminu Tambuwal ruwan duwqtsu a jihar Sakkwato.

An ce Tambuwal da ayarinsa na kan hanya daga wurin kamfe lokacin da aka farmake su, akalla motoci biyu lamarin ya shafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel