Surukin Ministan Buhari Ya Fice Daga Jam’iyyar APC Ya Koma Ta Adawa, PDP

Surukin Ministan Buhari Ya Fice Daga Jam’iyyar APC Ya Koma Ta Adawa, PDP

  • Jigon jam’iyyar APC mai ci kuma surukin ministan Buhari ya bayyana ficewa daga jam’iyyar APC, ya kama PDP
  • Zayyanu Wamakko ya kasance dan da ga tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aliyu Wamakko
  • Jam’iyyun siyasa na ci gaba da musayar mambobi yayin da zaben 2023 ke kara kusantowa nan da watanni

Jihar Sokoto - Zayyanu Wamakko, surukin ministan harkokin ‘yan sanda na Najeriya, Muhammad Maigari Dingyadi ya fice daga jam’iyyar APC zuwa ta PDP.

Zayyanu dan da ne ga shugaban jam’iyyar APC na jihar Sokoto, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, PM News ta ruwaito.

Ya bar jam’iyyar APC a lokacin da kamfen PDP a garinsu tsohon gwamnan a jiya Lahadi 1 ga watan Janairu 2023, a cewar wata sanarwa da Muhammad Bello, mai magana da yawun gwamna Tambuwal ya fitar.

Kara karanta wannan

2023: Abin da ya sa Mu ka Tsaida Bola Tinubu a Jam’iyyar APC Inji Sanatan Arewa

Dan sanata Wamakko ya koma PDP
Surukin Ministan Buhari Ya Fice Daga Jam’iyyar APC Ya Koma Ta Adawa, PDP | Hoto: Sokoto State Governor's Office
Asali: Facebook

Hakazalika, Zayyanu ya kasance shugaban jam’iyyar APC a yankin jihar, ya bayyana a gaban jama’a cewa, ya bar APC tare da komawa PDP ne bayan ganin kokari da kuma aiki tukuru na gwamna Tambuwal

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya bayyana cewa, ya ji sha’awar komawa PDP ne tare da dimbin magoya bayansa don gama kai a ci gaban da gwamnatin Tambuwal ta kawo.

Zan ba PDP gudunmawa don ci gaban jama’ar Sokoto

Ya kuma yi alkawarin ba da gudunmawa wajen burin jam’iyyar PDP wajen inganta rayuwar jama’ar jihar Sokoto, Politics Nigeria ta ruwaito.

Da yake magana a wurin taron, mataimakin gwamnan jihar, Manir Muhammad Dan Iya, wanda kuma shine abokin hamayyar Wamakko a takarar sanatan Sokoto ta Arewa ya ce yana da yakinin cin zabe a nan gaba kadan.

Kara karanta wannan

A Koreni Daga PDP Idan An Isa: Wike Ya Kalubalanci Uwar Jam'iyya

Duba da yadda tafiyar siyasar abokin hamayyar tasa, Dan iya ya ce zai lallasa Wamakko kafin karfe 12 na rana a ranar zabe.

Jiga-jigan PDP sun sauya sheka zuwa APC a jihar Katsina

A wani labarin kuma, jam'iyyar PDP ta yi rashi a karamar hukumar Mashi ta jihar Katsina, sun koma jam'iyyar APC mai mulki.

Wannan na fitowa ne daidai lokacin da jam'iyyun siyasa ke ci gaba da shirin babban zaben 2023 mai zuwa nan da wata da kwanaki kadan.

An ce wadannan daruruwan mambobin PDP sun sauya sheka ne a lokacin gangamin kamfen na dan takarar gwamnan APC, Dr. Dikko Radda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel