Gwamnonin APC 11, Sanatoci 37 Da Yan Majalisar Wakilai 15 Na Yiwa Atiku Aiki, Inji PDP

Gwamnonin APC 11, Sanatoci 37 Da Yan Majalisar Wakilai 15 Na Yiwa Atiku Aiki, Inji PDP

  • Daniel Bwala, kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP, ya bayyana cewa gwamnonin APC 11 na yiwa Atiku Abubakar aiki
  • Jigon na PDP ya kuma ce zuwa Disambar 20222, sanatoci 37 da yan majalisar wakilai 15 da aka zaba karkashin APC ne ke yiwa Atiku aiki
  • Atiku dan takarar shugaban kasa na PDP na fafatawa da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wajen neman darewa kujerar Buhari

Abuja - Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya bayyana cewa akalla gwamnonin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) 11 ne suke yiwa dan takararsa na shugaban kasa, Atiku Abubakar aiki.

Daniel Bwala, kakakin kwamitin ne ya bayyana hakan a wata hira da jaridar Daily Independent a ranar Lahadi, 1 ga watan Janairu.

Atiku da Tinubu
Gwamnonin APC 11, Sanatoci 37 Da Yan Majalisar Wakilai 15 Na Yiwa Atiku Aiki, Inji PDP Hoto: @atiku/@officialABAT
Asali: Facebook

Adadin gwamnoni, sanatoci da yan majalisar wakilai na APC da ke yiwa Atiku aiki ya bayyana

Kara karanta wannan

Tsagin Atiku Abubakar Ya Fadi Gaskiya Game da Babban Asirin da Wike Ya Bankado Kan Zaben 2003

Bwala ya kuma bayyana cewa, zuwa Disambar 2022, sanatoci 37 da yan majalisar wakilai 15 a APC suna aiki don ganin Atiku Abubakar ya lashe zaben shugaban kasa na 2023.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jawabinsa na cewa:

"A farkon makon Disamba, muna da gwamnonin APC 11 da suke goyon bayanmu kuma har yanzu akwai wasu a hanya. Muna da sanatocin APC 37 da yan majalisar wakilai 15. Wannan a makon farko na Disamba ne fa. Zuwa yanzu guda nawa kuke ganin mun sake samu."

Bwala ya fadi hakan ne yayin da yake martani ga ikirarin Kassim Afegbua, jigon APC da ya ce kimanin gwamnonin jam'iyyar 3 na yiwa Atiku Abubakar na APC aiki

Afegbua, tsohon kwamishinan labarai na jihar Edo ya yi zargin cewa yana da bayanan sirri cewa Atiku ya yi ganawar sirri da gwamnonin a Dubai.

Kara karanta wannan

Tambuwal Ya Fadi Wani Babban Aikin Buhari Da Atiku Zai Soke Da Zaran Ya Ci Zaben 2023

Atiku ya gana da gwamnonin APC a sirrince, Wike

A gefe guda, mun ji a baya cewa Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya zargi dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar da ganawa da wasu gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki a Dubai.

Wike ya ce hakan na daga cikin kokarin da Atiku ke yi na ganin gwamnonin sun dawo bayan shi tare da yi masa aiki gabannin babban zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel