Hadimin Atiku Ya Nemi Gwamna Wike Ya Baiwa Mutane Uku Hakuri Kan Kalamansa

Hadimin Atiku Ya Nemi Gwamna Wike Ya Baiwa Mutane Uku Hakuri Kan Kalamansa

  • Lamari ya kara dagulewa a babban jam'iyar adawa ta kasa PDP tsakanin bangaren Atiku Abubakar da gwamna Wike
  • Ana ci gaba da musayar zargi da tone-tonen wasu abubuwa da suka faru tun a zabukan da suka gabata kamar na 2003
  • Wike da sauran mambobin tawagarsa na G-5 sun kafe kan bakatarsu wacce har yanzun babu alamun za'a iya biya masu ita a PDP

Abuja - Phrank Shaibu, hadimin Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a inuwar PDP, ya bukaci gwamna Nyesom Wike ya nemi yafiyar tsohon mataimakin shugaban kasan.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa Mista Shaibu ya zargin Wike da faɗin, "Karya mara tushe," game da batun zaben shugaban kasa na shekarar 2003.

Gwamna Wike da Atiku.
Hadimin Atiku Ya Nemi Gwamna Wike Ya Baiwa Mutane Uku Hakuri Kan Kalamansa Hoto: thecable
Asali: UGC

A ranar Jumu'a, gwamna Wike ya yi ikirarin cewa sai da tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya duka har kasa ya roki Atiku ya bari ya nemi zango na biyu a mulki.

Kara karanta wannan

Tambuwal Ya Fadi Wani Babban Aikin Buhari Da Atiku Zai Soke Da Zaran Ya Ci Zaben 2023

A cewar Wike, tsohon mataimakin Obasanjon ya amince bisa sharaɗin a tsige Tony Anenih, babbam jigon PDP daga cikin kwamitin kamfe a wancan lokacin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Daya daga sharuddan da ya gindaya shi ne a tunbuke Tony Anenih daga kujerar Ministan ayyuka kuma kar a sanya sunansa a tawagar kamfe," inji Wike.

Gwamnan ya ce bisa tilas Obasanjo ya tsige Ministan daga makaminsa kuma ya zare shi daga cikin kwamitin yakin neman zabe.

Menene gaskiyar abinda ya faru?

Da yake martani a wata sanarwa ranar Asabar, Shaibu ya ce ba zai yuwu Wike ya ba da labarin abinda ya faru a wancan lokacin ba domin bai san komai ba.

Ya ce:

"Abun kunya ne ga Wike, a kokarin lullube karyarsa, ya nemi ruguza tarihin marigayi Chief Tony Anenih. har zuwa numfashinsa na karfe marigayi Anenih makunsanci ne ga Atiku."

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Babban Gwamnan PDP Yayi Ganawar Sirri Da Wike, Ortom a Fatakwal

"Bugu da gari alaka ce mai kyau tsakanin siyasar Marigayin da kuma ta Atiku Abubakar, saboda haka ya kamata Wike ya nemi afuwar Obasanjo, Atiku da iyalan Anenih."
"Obasanjo dattijon ƙasa ne, don haka rashin da'a ne Wike ya tsoma baki kan zamanin mulkinsa da kuma shafa wa Atiku Kashi sannan ya haɗa da kabarin marigayi Tony Anenih."

Akwai matsala da kuri'un Legas da Abuja

A wani labarin kuma Tinubu da Atiku Sun Gamu da Cikas, Miliyoyin Mutane a Abuja da Legas Ba Zasu Kada Kuri'a Ba a 2023

Saura kwana 55 zaben shugaban kasa, da yuwuwar mazauna Abuja da jihar Legas sama da miliyan biyu ba zasu samu damar jefa kuri'a ba. Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC ta ce ba gudu da ja da baya a sabbin tsarukan zamani da ta bullo da su don magance magudin zabe a 2023.

Kara karanta wannan

Rigimar PDP: Gwamna Wike Ya Sake Tona Wani Babban Sirrin Atiku

Asali: Legit.ng

Online view pixel