Zaben 2023: Takarar Atiku Na Fuskantar Gagarumin Barazana Yayin da Wike Ya Tona Wani Babban Sirrinsa

Zaben 2023: Takarar Atiku Na Fuskantar Gagarumin Barazana Yayin da Wike Ya Tona Wani Babban Sirrinsa

  • Gwamna Nyesom Wike yana nan a kan bakarsa don tabbatar da ganin tsarin shugabancin jam'iyyar PDP ya dawo daidai
  • Gwamnan na jihar Ribas ya nanata cewa bukatar gwamnonin G-5 na nan yadda yake kuma ba za yi masa kutse ba
  • Ya kuma bayyana cewa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na PDP na ta ganawar sirri da gwamnonin jam'iyya mai mulki

Rivers - Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya zargi Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da ganawa da wasu gwamnonin jam'iyyar All Progressive Congress (APC) cikin sirri duk a kokarinsa na janyo su bangarensa.

Gwamna Wike ya bayyana wannan sirrin a yayin kaddamar da aikin raba titin Eneka -Igbo Etche zuwa tagwayen hanya.

Atiku da Wike
Zaben 2023: Takarar Atiku Na Fuskantar Gagarumin Barazana Yayin da Wike Ya Tona Wani Babban Sirrinsa Hoto: Atiku Abubakar, Governor Nyesom Wike
Asali: Facebook

Jaridar The Cable ta nakalto Wike na cewa:

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Bayan Ganawa Da Tinubu, Sanatan Arewa Ya Aika Da Sako Mai Muhimmanci Ga Wike Ga Gwamonin G5

"Sun ce muna ta ganawa da sauransu. Menene matsalarku? Misali ace an yi wata ganbawa, shin Atiku bai ta ganawa da gwamnonin APC ba? Ku tambaye shi. Da yake Dubai, Ba mu san abun da ke gudana bane? Don haka, Me yasa kuka damu da zancenmu? G5 da kuka ce za ku iya lashe zabe babu mu, ku kyale mu."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A wajen kaddamar da aikin, Gwamna Wike ya kalubalanci manyan jiga-jigan PDP da ke kitsa korarsa daga jam'iyyar da su gwada su gani idan suna karfin aikata hakan.

Don karfafa barazanarsa, Gwamna Wike ya ce:

"Idan lokacin ya yi, za mu san wa ke da karfi da wanda bai da karfi."

Yayin da yake magana a taron, Gwamna Wike da Gwamnonin G-5 wadanda basa ga maciji da shugabancin PDP sun jaddada bukatarsu na neman Sanata Iyorchia Ayu ya sauka daga kujerarsa a matsayin shugaban jam'iyyar na kasa.

Kara karanta wannan

Ganawar sirri: Daga karshe bayani ya fito bayan ganawar Tinubu da gwamnonin PDP 5 a Landan

Gwamnonin na G-5 sun bore don tabbatar da ganin cewa dan kudu ya karbi ragamar shugabancin jam'iyyar don samar da daidaito, adalci da yi da kowa a jam'iyyar.

Kungiyar 'integrity group' da Gwamna Wike ke jagoranta ta ce ba zai yiwu dan takarar shugaban kasa da shugaban jam'iyyar na kasa su fito daga yanki daya ba, lamarin da kundin tsarin mulkin jam’iyyar ma ya kayyade.

Yadda Obasanjo ya durkusa ya roki Atiku saboda ya zarce - Gwamna Wike

Kamar yadda jaridar PM News ta rahoto, Wike ya kuma bayyana yadda wani lamari ya wakana tsakanin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da mataimakinsa na lokacin Atiku Abubakar tsakanin 2002 da 2003.

Gwamnan na jihar Ribas ya bayyana cewa Obasanjo ya duka a kan gwiwowinsa don ya roki Atiku don marawa kudirinsa na zarcewa baya yayin da Atiku ya bashi sharadi.

Gwamna Wike ya ce:

"Kun ce muna bayar da sharadi, amma kun manta tarihi. A 2002-2003 lokacin da shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya so zarcewa, ya tsuguna a gaban mataimakinsa sannan ya ce mataimakina dan Allah ka bari na yi takara.

Kara karanta wannan

2023: Fitaccen Gwamnan Arewa Ya Dau Alkawarin Gina Masallaci da Coci a Wani Kauye

"Kun san daya daga cikin sharadan da ya bashi, dole a tsige Tony Anenih a matsayin ministan ayyuka sannan dole a cire Tony Anenih a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa. Obasanjo ya bi sannan ya tsige Tony Anenih a matsayin ministan ayyuka ya kuma cire shi daga kwamitin yakin neman zabe."

Gwamnonin G-5 sun gabatarwa Tinubu da bukatarsu

A wani labarin, mun ji cewa gwamnonin G-5 sun nemi goyon bayan dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu a jihohinsu.

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, gwamnonin na PDP da basa tare da Atiku su na so Bola Tinubu ya goyi bayan ‘yan takaransu a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel