Atiku Zai Bude Boda Idan Ya Zama Magajin Buhari a 2023, Tambuwal

Atiku Zai Bude Boda Idan Ya Zama Magajin Buhari a 2023, Tambuwal

  • Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal ya bayyana manyan ayyukan da Atiku Abubakar zai yiwa yan Najeriya idan ya lashe zabe a 2023
  • Tambuwal ya bayar da tabbacin cewa dan takarar shugaban kasa na PDP zai sake bude boda idan ya zama magajin Buhari a zabe mai zuwa
  • Darakta janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasar na PDP ya kuma tausayawa al'ummar yankin Illela kan hare-haren yan bindiga

Sokoto - Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya bayyana cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar, zai sake bude iyakokin kasar idan aka zabe shi a 2023.

Tambuwal, wanda shine darakta janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP ya yi hasashen ne a ranar Asabar, 31 ga watan Disamba, a wajen gangamin yakin neman zaben jam'iyyar a karamar hukumar Illela da ke jihar.

Kara karanta wannan

Fitattun Yan Najeriya a Turai Sun Daukar Wa Atiku Gagarumin Alkawari Gabannin 2023

Atiku da Tambuwal
Atiku Zai Bude Boda Idan Ya Zama Magajin Buhari a 2023, Tambuwal Hoo: Atiku Abubakar/Aminu Waziri Tambuwal
Asali: Facebook

A cewar gwamnan, dan takarar shugaban kasar na PDP ya yi wa kasar tanadi na musamman, jaridar Vanguard ta rahoto.

Tambuwal ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Wadannan sun hada da sake bude iyakokin kasar, magance matsalolin rashin tsaro da samawa yan Najeriya muhimman abubuwan da suke bukata na rayuwa."

Gwamnan ya kara da cewar gwamnatinsa a jihar tana matukar tausayawa mutanen yankin Illela kan kasancewarsu cikin yankunan da yan bindiga suka fi kaddamar da hare-hare.

Ya kara da cewa:

Duk da matsalolin rashin tsaro, koma bayan tattalin arziki da illar annobar korona, mun aiwatar da ayyuka da dama a bangaren kiwon lafiya, ilimi, samar da ruwa da shirin tallafi da sauransu."

A nashi jawabin, Darakta Janar na kwamitin yakin neman zabe a Sokoto, Alhaji Yusuf Sulaiman, ya bukaci mutanen yakin da su zabi PDP don ci gaban aiki, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Rigimar PDP: Gwamna Wike Ya Sake Tona Wani Babban Sirrin Atiku

Gwamnatina za ta mayar da hankali wajen aikin kasuwar Illela idan na ci zabe, dan takarar gwamnan PDP

Malam Sa'idu Umar, dan takarar gwamnan PDP ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankali sosai wajen aikin gina kasuwar kasa da kasa a Illela idan har aka zabe shi.

Hakazaika, Umar ya ce zai ba daukacin mutanen jihar Sokoto kulawa ta musamman.

Ya yi alkawarin dorawa daga inda Tambuwal ya tsaya sannan ya aiwatar da ayyukan ci gaba da dama idan aka zabe shi.

Rikicin PDP: Ayu ya saka wando daya da gwamnonin G5

A wani labarin kuma, shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu ya kara saka wando daya da gwamnonin G5 karkashin jagorancin Nyesom Wike na jihar Ribas.

Ayu ya soke jerin sunayen da tsagin Wike suka aika sakatariyar PDP na kasa domin zama wakilan jam'iyyar a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel