PDP Ta Fallasa ‘Umarnin’ da Bola Tinubu Ya ba ‘Yan APC da Aka Yi Taron Sirri a Landan

PDP Ta Fallasa ‘Umarnin’ da Bola Tinubu Ya ba ‘Yan APC da Aka Yi Taron Sirri a Landan

  • Hon. Debo Ologunagba ya kira taron ‘yan jarida, inda ya ce sun gano jam’iyyar APC na neman wargaza zabe
  • Sakataren yada labaran PDP na kasa ya zargi Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da bada umarnin a tada rikici
  • Ologunagba yake cewa a dalilin wannan umarni ne aka fara ganin ana kai wa ofishin INEC hare-hare a Najeriya

Abuja - Jam’iyyar hamayya ta PDP ta ankarar da jama’a game da abin da ta kira gano shiryayyen yunkurin kawowa zaben 2023 matsala a Najeriya.

Vanguard ta ce Sakataren yada labaran PDP, Debo Ologunagba ya kira taron menama labarai, ya ce ba kowa yake wannan aikin ba sai jam’iyyar APC.

Hon. Debo Ologunagba ya sanar da ‘yan jarida a garin Abuja a ranar Laraba cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bada umarni ayi amfani da karfi.

Kara karanta wannan

Ana Yi Wa Rayuwata Barazana Saboda Na Kai Jam’iyyar APC Kotu – ‘Dan Takara

A cewar PDP, ‘dan takaran shugaban kasar jam’iyya mai mulki ya fahimci ba za su samu karbuwa a 2023 ba, sai suka fara shirin yi wa jama’a dole.

Kakakin na PDP ya ce Bola Tinubu ya yi wani taro a Landan, a nan ya yi kira ga ‘ya ‘yan jam’iyyarsa su yi amfani da rigima domin cin zaben badi.

Jawabin Hon. Debo Ologunagba

“Mun kira ku yau ne domin a ankarar da Najeriya da kasashen Duniya game da shirin da makiyan tsarin farar hula suke yi na hargitsa zaben 2023.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bola Tinubu
Bola Tinubu a taron jama'a Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook
Mu na ankarar da ‘Yan Najeriya kan umarnin ‘dan takaran shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ga mutanensa na yin amfani da karfi.
APC ta fahimci ba a goyon bayanta, ta fara tada rigima domin kawo matsala a zaben da za ayi.

Kara karanta wannan

‘Dan takaran LP Ya Fito Ya Fadi Yadda Za a Raba Kan Arewa, Peter Obi Ya Dare Mulki

'Yan Najeriya za su iya tuna yadda Tinubu ya yi taro a bayan labule a Landan a farkon watan nan, yana fadawa ‘yan jam’iyyarsa ba a bada mulki a sama."

- Hon. Debo Ologunagba

'Umarnin' Tinubu ya fara aiki - PDP

An rahoto Ologunagba yana mai cewa a dalilin wannan umarni da ‘dan takaran na APC ya bada, ‘ya ‘yan jam’iyyarsa sun fara tada rigima a wasu jihohi.

Daga cikin tada zaune-tsayen ne jam’iyyar PDP ta ce aka kai wa ofisoshin hukumar INEC a Ogun, Osun da Imo, kuma ana shirin kai hari a Kofi da Delta.

Baya ga haka, sakataren yada labaran na PDP ya zargi jam’iyyar APC da biyan kudi wajen sayen katin PVC da kuma lalata na’urorin aikin hukumar INEC.

PDP tayi babban rashi wajen kamfe

Dazu aka ji labari wani jigon jam'iyyar PDP a jihar abokin gamin takarar Atiku watau Delta, Chief Onuame, ya mutu a hanyar zuwa wurin gangamin kamfe.

Kara karanta wannan

Shugaban Jam’iyya da ya yi Murabus ya Hango Makomar Kwankwaso, NNPP a 2023

Bayanai sun nuna cewa motarsa ta yi taho mu gama da tankar dakon fetur, nan take direbansa ya cika a wurin. Wannan babban rashi ne ga takarar PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel