Ana Yi Wa Rayuwata Barazana Saboda Na Kai Jam’iyyar APC Kotu – ‘Dan Takara

Ana Yi Wa Rayuwata Barazana Saboda Na Kai Jam’iyyar APC Kotu – ‘Dan Takara

  • Wani da ya nemi zama ‘dan takaran kujerar majalisar dokoki a Ohakwu ya ce ana neman kashe shi
  • Ejike Agbo ya kira taron manema labarai, ya shaida masu barazanar da shi da iyalinsa suke fuskanta
  • ‘Dan siyasar yana ganin zuwa kotu da ya yi domin karbe takara a jam’iyyar APC ya jefa shi a matsala

Ebonyi - Ejike Agbo wanda za a iya sa shi a cikin jagororin jam’iyyar APC a jihar Ebonyi, ya yi bayanin irin halin da ya samu kan shi a yanzu.

Vanguard ta rahoto Ejike Agbo yana cewa wasu mutane ‘yan jam’iyyarsu ta APC su na yi wa rayuwarsa barazana saboda ya kai kara gaban Alkali.

‘Dan takaran kujerar majalisar dokokin ya ce wasu da bai san su ba, su na aiko masa da sako a dalilin kalubalatar zaben tsaida gwanin APC da ya yi.

Kara karanta wannan

Zabe ya karaso, Hukumar INEC ta Jero Manyan Abubuwa 2 da take Tsoro a 2023

Agbo mai neman wakiltar Ohaukwu ta kudu a majalisar dokokin jiha ya ce tun bayan zaben tsaida ‘dan takara na jam’iyyar APC, aka sace masa mota.

Sharrin abokan gaba ne - 'Yan sanda

Tun da aka sace masa mota a wajen wani taron masu ruwa da tsaki a Enugu, har yau babu labarin inda motar ta shiga, duk da ana ta kokarin gano ta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da aka je wajen ‘yan sanda, ‘dan takaran ya ce jami’an tsaron sun sanar da shi ya hakura da motar, aka fada masa bacewar na da alaka da siyasa.

Ejike Agbo
‘Dan Takaran APC, Ejike Agbo Hoto: APC Updates
Asali: Twitter
"Ina so duk Duniya su san abin da ke faruwa, ni da iyalina mu na fuskantar barazana. Saboda matsalar da ake fama da ita, mutum ba zai yi wasa ba.
Su na son hada mani tarko, a taso ni a gaba saboda ra’ayi na ya sha ban-bam da na masu mulki, domin na je kotu kan sakamakon zaben tsaida gwani."

Kara karanta wannan

Shugaban Jam’iyya da ya yi Murabus ya Hango Makomar Kwankwaso, NNPP a 2023

- Ejike Agbo

A cewar Ejike Agbo, kullum wayar salularsa cikin ganin kira daga boyayyun lambobi take, ana yi wa shi da iyalinsa barazana, ana cewa za a hallaka shi.

Abin ya kai jigon na APC ya ce ana kokarin nemansa da sharri, a gurfanar da shi a kotu a boye, don haka ne ya yi kira ga ‘yan sanda su ba shi kariya.

‘Dan siyasar ya yi wadannan bayanai lokacin da ya kira taron menema labarai a Abakaliki.

LP za ta ci zabe a 2023

An ji labari cewa lissafin da wasu magoya bayan Peter Obi suke yi shi ne, Rabiu Musa Kwankwaso zai birkita lissafin PDP da APC a Arewa a NNPP.

Peter Ahmeh ya ce idan aka je Kudancin Najeriya, Obi zai hana PDP sakat, sannan jam’iyyar NNPP ba za ta iya samun karbuwa a jihohin yankin ba.

Kara karanta wannan

Sanatan Arewa Ya Ba Tinubu Gudumuwar Motoci 100 Domin Ayi Kamfe da Kyau

Asali: Legit.ng

Online view pixel