‘Dan takaran LP Ya Fito Ya Fadi Yadda Za a Raba Kan Arewa, Peter Obi Ya Dare Mulki

‘Dan takaran LP Ya Fito Ya Fadi Yadda Za a Raba Kan Arewa, Peter Obi Ya Dare Mulki

  • Peter Obi zai doke jam’iyyun APC da PDP a zaben Shugaban kasa a karkashin inuwar LP a 2023
  • Wannan shi ne ra’ayin Peter Ameh, a cewarsa alamu sun nuna nasarar jam’iyyar LP a zabe mai zuwa
  • Ameh ya ce takarar Rabiu Kwankwaso a jam’iyyar NNPP za ta raba kuri’un PDP da APC da ke Arewa

Abuja - Peter Ameh wani ‘dan siyasa mai tasowa a Najeriya, ya yi hira da Sun, inda aka yi masa tambaya a game da abin da ya shafi zaben 2023.

Peter Ameh yana takarar kujerar majalisar tarayya a jihar Kogi, kuma yana cikin shugabannin majalisar IPAC, sannan shugaban jam’iyya ne shi.

A hasashensa, zaben 2023 zai sha bambam da na baya saboda INEC ta fito da na’urar BVAS da kafar IReV, kuma an samu sababbin fuskoki a siyasa.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa a 2023: APC da PDP Sun Mutu Murus, Ni Za Ku Zaba, Kwankwaso Ga Yan Najeriya

Ameh yake cewa Peter Obi ne zai yi nasara, ya ce idan ya fadi haka ana ganin ya yi son-kai, amma alkaluma sun nuna nasarar jam’iyyar hamayyar.

A 2023, Ibo ba za su zabi PDP ba - Ameh

Yanzu maganar da ake yi, ‘dan siyasar ya ce jam’iyyar PDP ba za ta lashe zabe a Jihohin Kudu maso gabas ba, akasin abin da aka saba tun a 1999.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yankin Arewa kuwa, Ameh ya ce Rabiu Musa Kwankwaso zai raba kuri’un jam’iyyun PDP da APC, amma ba zai tsira da komai a jihohin Kudu ba.

‘Dan takaran NNPP
Rabiu Kwankwaso da Nyesom Wike Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

LP za ta tashi da kuri'u a Arewa

Ameh ya shaidawa jaridar cewa jam’iyyar LP za ta samu kuri’u masu yawa a jihohin Kano da Jigawa domin ta tsaida ‘yan takaran da suke da farin jini.

Tsaida Yusuf Datti Baba Ahmed a matsayin abokin takarar Peter Obi a jam’iyyar zai taimakawa LP wajen samun kuri’u a jihohin Arewa, a ra’ayin Ameh.

Kara karanta wannan

Shugaban Jam’iyya da ya yi Murabus ya Hango Makomar Kwankwaso, NNPP a 2023

"A can jihohin Arewa, Kwankwaso yana nan zai raba kuri’un da ya kamata APC da PDP su samu. Shi zai lashe su, amma ba za su yi masa tasiri ba.
(Kwankwaso) bai da mutane a Kudu maso gabas, Kudu maso yamma, Kudu maso kudu da Arewa ta tsakiya. Wannan zai taimakawa jam’iyyar LP.
Babu wanda ya isa ya samu kuri’u miliyan biyu daga Kano domin Kwankwaso zai bata wannan lissafi, za su raba kuri’u tare da PDP da kuma APC.
LP kuma za a samu wasu kuri’un da ke Kano. Idan ka je Jigawa, LP ta na da ‘yan takara masu karfi da suke neman mulki, haka a jihar Kano.
Yanzu babu wadannan kuri’un da APC take samu, babu wani mai gardama, Obi ne yake kan gaba a zaben nan, rabu da maganar PDP da APC.

- Peter Ameh

Tinubu zai kai labari a Jigawa?

Da jirgin yakin neman zaben APC ya ziyarci karamar hukumar Malammadori, an ji labari Gwamnan Jigawa ya fadawa mutanensa amfanin APC.

Kara karanta wannan

Hamza Al-Mustapha da Wasu ‘Yan Takara da Ya Kamata a Lura da Su da Kyau a 2023

Idan Bola Tinubu ya kafa Gwamnati a Najeriya, Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya ce za a gano fetur da yake kwance a Jihar Jigawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel