Zaben 2023: Tinubu, Atiku, Obi, Da Wasu Suna Cikin Matsala Yayin Da INEC Ta Fitar Da Sabbin Ka'idoji

Zaben 2023: Tinubu, Atiku, Obi, Da Wasu Suna Cikin Matsala Yayin Da INEC Ta Fitar Da Sabbin Ka'idoji

  • Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta fitar sa sabbin ka'idoji da ya dakatar da jam'iyyu da yan siyasa daga yin wasu abubuwa
  • Sabbin dokokin sun gargadi jam'iyyun siyasa da yan takara kada su yi kamfen a hukumomin gwamnati da wuraren ibada
  • INEC ta kuma ce kada yan takara da jam'iyyun siyasa su karbi gudunmawa da ya haura Naira miliyan 50

FCT, Abuja - Gabanin babban zaben shekarar 2023, Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta gargadi yan takara da yan siyasa su dena kamfen a wuraren ibada da hukumomin gwamnati.

Kazalika, an kayyade Naira miliyan 50 a matsayin kudi mafi yawa da daidaikun mutane ko kungiya za su iya bawa dan takara.

Mahmood Yakubu
Zaben 2023: Tinubu, Atiku, Obi, Da Wasu Suna Cikin Matsala Yayin Da INEC Ta Fitar Da Sabbin Ka'idoji. Hoto: INEC.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: PDP ta shiga ta fita, ta sa an soke zaben kananan hukumomi da aka gudanar a wata jiha

Hakan na kunshe ne cikin sanarwar da INEC ta fitar a Abuja ta hannun kwamishinanta kuma direkta na kwamitin labarai da wayar da kan masu zabe, Festus Okoye.

Bisa wannan ka'idojin, hukumar za ta rika saka ido sosai kan yan takarar shugaban kasa kamar Atiku Abubakar, Bola Tinubu da Peter Obi.

Kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto, Okoye ya bayyana cewa ana tattauna game da sabbin ka'idojin.

Ya ce hukumar ta amince da sabbin ka'idojin, wacce ke dauke da sanarwa kan yin ralli, taruka da kamfen.

Okoye ya ce an dora dukkan sabbin dokokin zaben a shafin yanar gizo na hukumar, kuma za a bawa jam'iyyun siyasa, kungiyoyin cigaban al'ummma, yan jarida da sauran masu ruwa da tsaki kwafinsu.

Okoye ya bayyana cewa hukumar za ta yi aiki bisa tanadin sabon dokar zabe ta 2022 (da aka yi wa kwaskwarima) dangane da bawa jam'iyyun siyasa tallafi.

Kara karanta wannan

Alkawari kaya: Tinubu ya fadi yadda zai yi da 'yan IPOB idan ya gaji Buhari a 2023

Kamar yadda Vanguard ta rahoto, an bukaci yan takara su kiyayye dokokin da dokar zabe ta bada yayin yin kamfen dinsu.

Okoye ya ce:

"Kudaden da jam'iyyar siyasa za ta kashe ya kasu kashi uku; na kula da yan takara da zaben fidda gwani; na kula da yan takara da yin zabuka; kuma, na sauran abubuwa da za su iya tasowa yayin zabe."

Tinubu Ya Soki Peter Obi da Atiku a Taron Bude Kamfen Din APC a Jos

Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, ya soki abokan hamayyarsa na jam'iyyun LP da PDP a taron da APC ta gudanar a jihar Filato.

Tsohon gwamnan na Legas ya ragargaji Atiku, kana ya tabo tsohon gwamnan jihar Anambra; Peter Obi a cikin jama'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel