Kotu Ta Soke Zaben Kananan Hukumoni da Aka Gudanar a Jihar Osun

Kotu Ta Soke Zaben Kananan Hukumoni da Aka Gudanar a Jihar Osun

  • An samu tsaiko a jihar Ogun yayin da kotu ta rushe zaben da aka gudanar na kananan hukumomi saboda wasu dalilai
  • An ruwaito cewa, jam'iyyar APC ce kadai ta samu halartar zaben, lamarin da bai yiwa jam'iyyar adawa ta PDP dadi ba
  • Da yake yanke hukunci, mai shari'a ya bayyana abin da ya yi la'akari dashi wajen soke zaben gaba dayansa na kananan hukumomi 30 a jihar

Jihar Osun - Wata kotun tarayya mai zamanta a Osogbo, babban birnin jihar Osun a ranar Juma'a ta soke zaben kananan hukumomi da hukumar zabe mai zamanta ta jihar ta gudanar a ranar 15 ga watan Oktoba a jihar Osun, Punch ta ruwaito.

A hukuncin da ya yanke, mai shari'a Nathaniel Ayo-Emmanuel ya ce, yin zaben ya saba da sashe na 29 da 32 da kundin zaben 2022.

Kara karanta wannan

Alkawari kaya: Tinubu ya fadi yadda zai yi da 'yan IPOB idan ya gaji Buhari a 2023

A tun farko, jam'iyyar PDP ce ta tunkari kotu tare da neman a hana hukumar zabe bari a yi zaben kamar yadda aka tsara.

Kotu ta soke zaben kananan hukumomi a jihar Osun
Kotu Ta Soke Zaben Kananan Hukumoni da Aka Gudanar a Jihar Osun | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Sauran wadanda aka hada a karar da PDP ta shigar sun hada da jam'iyyar APC da shugabanta na wancan lokacin, Adeboyega Famoodun.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda zaben ya kasance

A zaben da aka gudanar, jam'iyyar APC ce ta cinye dukkan kujerun kananan hukumomi 30 a jihar, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kafin zaben, shugaban hukumar zaben jihar, Segun Oladitan ya sanar da cewa, jam'iyya daya ce kadai ta nuna sha'awar shiga zaben da aka gudanar.

Sai dai, bai bayyana sunan jam'iyyar da ta ta nuna sha'awa da shiga zaben ba a loakcin sai daga baya.

An ruwaito cewa, kuri'un da aka yi amfani dasu ba sa dauke da tambarin jam'iyya, kawai suna dauke da rubutun 'Yes' or 'No', wato 'Eh' ko 'Aa' a jikinsu.

Kara karanta wannan

Ganduje Ya Kaddamar da Gangamin Kamfen din APC a Gaya

Wannan lamari ya girgiza PDP, don haka ta nemi a kwaci hakkinta daga hukumar a gaban kotu.

Ba wannan ne karon farko da kotu ke rusa zabe ba a Najeriya, an soke zaben fidda gwanin gwamnan jihar Ribas a jam'iyyar APC da aka gudanar a watannin baya.

Mai shari'a ya soke zaben ne duba da hujjojin da suka bayyana a gabansa yayin bincike kan karar da aka shigar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel