Tinubu Ya Caccaki Peter Obi da Atiku a Taron Bude Gangamin Kamfen APC a Jos

Tinubu Ya Caccaki Peter Obi da Atiku a Taron Bude Gangamin Kamfen APC a Jos

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya caccaki abokan hamayyarsa gabanin zaben 2023 mai zuwa
  • Tinubu ya ce, Atiku da Tinubu na amfani da sarkafaffun sunaye da manufarsu kuskure ne, don haka ya ce ya fi su cancanta
  • A yau ne aka kaddamar kamfen na jam'iyyar APC a Najeriya a birnin Jos ta jihar Filato, Arewa ta Tsakiya a Najeriya

Jos, jihar Filato - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya caccaki abokan hamayyarsa daga jam'iyyun Labour da PDP a taron da APC ta gudanar a jihar Filato.

Tinubu ya caccaki Atiku Abubakar, kana ya tabo tsohon gwamnan jihar Anambra; Peter Obi a bainar jama'a.

Ya bayyana sukar su ne a Jos ranar Talata yayin da yake kaddamar kamfen dinsa, a taron da ya samu halartar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Tinubu Ya Nuna Bajintarsa Ta Rawar Da Ba A Saba Gani Ba Yayin Da APC Ta Kaddamar Da Kamfen A Filato

Hakazalika, rahoton jaridar Leadership ya bayyaa cewa, gwamnoni 10 na APC ne suka hallara tare da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan da tsoffin gwamnoni da dai sauran jiga-jigan gwamnatin kasar nan.

Atiku da Obi suna kan kuskure, inji Bola Tinubu

A cewar Tinubu, kirarin da Atiku yake amfani dashi na 'Atikulated' kuskure ne, yayin da 'Obi-dients' na 'yan a mutun Peter Obi kuwa babban kuskure kuma bata.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kuma soki Peter Obi da cewa:

"Peter Obi a Legas yake rayuwa. Bai san hanyar zuwa Anambra ba."

'Yan siyasa a Najeriya na ci gaba da musayar yawu tare da caccakar juna tun bayan da aka buga gangar siyasa a shirin zaben 2023.

Naija News ta yada cikakken jawabin da Tinubu ya gabatar a filin taron gangamin da aka gudanar a Jos.

Kara karanta wannan

Kamfen Tinubu: Gwamna ya fadi dalilin da yasa APC ta fara kamfen dinta a jihar Filato

Zan nemi a yafewa Najeriya bashi idan na gaji Buhari, inji Atiku

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana matsayarsa da inda ya dosa kan ci gaban tattalin arzikin Najeriya.

Atiku ya ce zai yi kokarin tabbatar da an yafewa Najeriya bashin da ake binta, ya fadi hanyoyin da zai bi wajen tabbatar da wannar manufa tasa.

Ya kuma bayyana cewa, zai yi duk mai yiwuwa don tabbatar da tattalin arzikin Najeriya ya habaka cikin kankanin lokaci kamar yadda jam'iyyar PDP ta yi a mulkinta na farko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel