Karin Bayani: Kotu Ta Haramtawa Dan Takarar Gwamnan Jihar Ribas Na APC Yin Takara

Karin Bayani: Kotu Ta Haramtawa Dan Takarar Gwamnan Jihar Ribas Na APC Yin Takara

  • Kotun tarayya mai zama a jihar Ribas ta soke zaben fidda gwanin APC a jihar saboda wasu dalilai da ta yi la'akari dasu
  • Wannan na zuwa ne bayan da jam'iyyar PDP ta shigar da kara don kalubalantar ingancin zaben da aka gudanar a APC
  • Kotu ta sake soke zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP a jihar Zamfara bayan da aka daukaka kara zuwa gaba

Kotun tarayya mai zamanta a Fatakwal ta haramtawa dan takarar gwamnan jihar Ribas a jam'iyyar APC, Tonye Cole yin takara a zaben badi.

Haramtawa Cole tara na zuwa ne saboda karar da aka shigar kan zamansa mai mallakar takardar zama dan kasashe biyu mabambanta.

Rahoton jaridar The Nation ya bayyana cewa, Cole na da takardar zama dan kasar Burtaniya da na Najeriya.

Kotu ta haramtawa dan takarar APC yin takarar gwamna a jihar Ribas
Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Haramtawa Dan Takarar Gwamnan Jihar Ribas Na APC Yin Takara | Hoto: thecable.bg
Asali: UGC

Yadda ya lashe zaben fidda gwanin APC da aka gudanar

A watan Mayun 2022, Cole, wanda shine shugaban kamfanin Sahara Group ya lashe tikitin takarar gwamna a jihar Ribas, TheCable ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cole ya banke abokin hamayyarsa, Ojukai Flagamakere, inda ya samu kuri'u 986, Ojuki kuwa ya samu kuri'u 190 kacal.

Sauran 'yan takarar sun hada da Sukonte Davids mai kuri'u 49, Michael West mai kuri'u 43 da Benald Miku mai kuri'u biyu sai kuma Magnus Abe da ya samu kuri'a daya kacal.

A bangare guda, jam'iyyar PDP ta jihar Ribas ta tunkari kotu domin kalubalantar zaben fidda gwanin bisa zargin deliget-deliget da suka kada kuri'u a zaben basu cancanta ba kwata-kwata.

Ba wannan ne karon farko da kotu ta soke zaben fidda gwani a wata jiha ba a Najeriya, hakan ya faru a jihohi da yawa a kasar.

An sake soke zaben fidda gwanin PDP a jihar Zamfara

A wani labarin na daban, kun ji cewa, an sake soke zaben fidda gwanin PDP a jihar Zamfara, wanda ya samar da Dauda Lawal a matsayin dan takarar gwamna.

Wannan na zuwa ne bayan sake daga karar da aka yi a baya na kalubalantar hukuncin da aka yi na soke zaben tare da sake shi a cikin kwanaki.

Jam'iyyun siyas a kasar nan na ci gaba da fuskantar kalubalen rikicin cikin gida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel