APC ta Kaddamar da Kamfen a Garin Manyan ‘Yan Hamayya a Kano

APC ta Kaddamar da Kamfen a Garin Manyan ‘Yan Hamayya a Kano

  • Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya kaddamar da gangamin yakin neman zaben Nasiru Gawuna matsayin Gwamnan Kano a zaben 2023
  • An kaddamar da kamfen din a karamar hukumar Gaya ta jihar Kano, inda babbar jam’iyyar hamayya ta NNPP ke da tsananin mabiya a Kano
  • Manyan ‘yan siyasa na jihar Kano a suka sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP tare da mabiyansu, wanda babban kalubale ne ga jam’iyy mai mulki

Kano - A ranar Laraba, ‘dan takarar gwamnan jihar Kano a karkashin jam’iyyar APC, Nasir Gawuna, ya kaddamar da yakin neman zabensa a karamar hukumar Gaya, yankin da jam’iyyar adawa ta NNPP ke da matukar tasiri, Premium Times ta rahoto.

Gwamna Abdullahi Ganduje
APC ta Kaddamar da Kamfen a Garin Manyan ‘Yan Hamayya a Kano. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Kamfen din da aka kaddamar a Gaya, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne jihar Kano ne ya jagoranta tare da wasu manyan mambobin jam’iyyar inda suka kwana a dakin taron garin suna ganawa da manyan jam’iyyar na yankin da masu fadi a ji.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kotun Daukaka Kara Ta Dawowa Binani Takararta ta Gwamnan Adamawa a APC

A yayin jawabi ga taron, Gawuna yace da taimakon Allah da kuma jama’ar jihar, zai yi nasara a zaben.

“Tun bayan da na tabbata ‘dan takarar gwamnan jihar, na mika takara ta ga Allah mai girma inda na sakankance cewa ba zai bar ni a hanyar da bata dace ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Idan aka zabe ni, ina fatan Allah zai min jagoranci ga hanya madaidaiciya.”

- Gawuna yace.

Gawuna yayi kira ga masu kada kuri’u da su zabi ‘yan takarar APC a dukkan fadin jihar. Yayi alkawarin cewa ‘yan takarar APC ba zasu ba jama’a kunya ba idan aka zabe su.

Yanki mai wahala

Jaridar Punch ta rahoto cewa, Gaya karamar hukuma ce dake da girma a mazabar Kano ta kudu wacce ta hada da kananan hukumomi 16 a yankin. Tana daya daga cikin yankunan da APC zasu fafata da NNPP.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Ko Da Tsiya-Tsiya Sai Mun Lashe Zabe Gwamnan Kano: Shugaban APC, Abdullahi Abbas

Jam’iyyar APC ta tsayar da Kabiru Gaya matsayin ‘dan takarar sanatan yankin. Tauraruwar Gaya ta rage haske a yankin bayan mazauna yankin sun kushe gadar sama ta wucewar jama’a da ya so yi. Sun ce sun fi son ruwan sha.

Gaya na fuskantar hamayya daga Kawu Sumaila, ‘dan takarar sanatan yankin a jam’iyyar NNPP tare da Abdulmumin Jibrin, tsohon ‘dan majalisar wakilai, Kabiru Rurum, tsohon kakakin majalisa kuma ‘dan majalisa mai ci a yanzu daga yankin, duk sun koma NNPP.

Mutum 23 sun yanke jiki sun fadi a gangamin goyon bayan Tinubu

A wani labari na daban, mutane 23 ne suka yanke jiki suka fadi sakamakon cunkoson da aka samu a gangamin goyon bayan Bola Tinubu a Kano.

Masu taimakon gaggawa da jami’an tsaro ne suka dinga mai dauki ga wadanda lamarin ya ritsa dasu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel