Rikicin PDP da Ke Faruwa a Filato Mu Kam Alheri Ne a Gare Mu, Inji APC

Rikicin PDP da Ke Faruwa a Filato Mu Kam Alheri Ne a Gare Mu, Inji APC

  • Jam'iyyar APC a jihar Filato ya bayyana jin dadinta da yadda rikicin cikin gida ke kara dabaibaye jam'iyyar adawa ta PDP
  • Wata kungiyar jam'iyyar PDP mai goyon bayan Atiku ta barranta da tsohon gwamnan jihar, David Jonah Jang
  • Gwamna Nyesom Wike na ci gaba da bayyana adawarsa ga shugabancin jam'iyyar PDP, lamarin da ke kara kunno rikici a jam'iyyar

Jihar Filato - Jam'iyyar APC a jihar Filato ta bayyana cewa, karin rikicin gida da jam'iyyar PDP ke fuskanta alheri ne gare ta saboda hakan zai kara kaimin nasararta a zaben 2023 mai zuwa.

Daily Trust ta ruwaito cewa, kungiyar goyon bayan Atiku a Filato mai suna Plateau for Atiku Movement (PAM) a ranar Talata ta yi taron 'yan jarida don nuna barranta da tsohon gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Na Hannun Daman Buhari Ya Shiga Kungiyar Gwamnonin G5, Ya Kulla Yarjejeniya Da Wike

Kungiyar ta bayyana rashin goyon bayanta ga Jonah David Jang ne bisa zargin ya koma tsagin gwamna Nyesom Wike mai adawa da Atiku.

Gwamna Wike na ci gaba da bayyana adawarsa ga dan takarar shugaban kas ana jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar tare da neman a tsige shugaban PDP na kasa Iyochia Ayu.

Rikicin PDP alheri ne a garemu, inji APC
Rikicin PDP da Ke Faruwa a Filato Mu Kam Alheri Ne a Gare Mu, Inji APC | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A taron da kungiyar ta gudanar tare da jagorancin Istifanus Mwansat ta ce, Jang ya basu kunya wajen juyawa Atiku baya tare da bin sahun Wike.

Gwamna Wike dai na ci gaba da bayyana cewa, a shirye yake da 'yan tawagarsa don su tattauna da kuma yin sulhu da shugabannin PDP, Vanguard ta ruwaito.

Mun ji dadi, ba mu ji dadi ba

A bangarenta, APC ta ce hakan ya yi mata dadi, inda sakataren yada labaranta Sylvanus Namang yace nan gaba kadan mambobin PDP za su samu rabuwar kai.

Kara karanta wannan

Atiku ya shiga tasku, kungiyar matasan da PDP ke ji da ita ta koma goyon bayan wani dan takara

A cewarsa:

"Jang ne mamallakin PDP saboda tsarin komai shi ke tafiyar dashi. Saboda haka, don sun nuna rashin goyon bayansa hakan zai dagula lamari ne kawai.
Ba zan ce mun ji dadin haka ba saboda muna son abokan hamayya masu karfi, amma ta wata hanyar muna jin dadi saboda za mu nasara cikin sauki."

Shugabannin wata kungiyar PDP sun koma APC

Ana cikin irin wannan yanayin, wasu jiga-jigan PDP suka bayyana komawarsu jam'iyyar APC mai mulki saboda wasu dalilai nasu.

Wannan na zuwa ne jim kadan bayan fara gangamin kamfen na zaben 2023 da dukkan jam'iyyun siyasar suka fara a watan jiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel