Kungiyar Matasa Masu Tallata Atiku Sun Sauya Sheka, Sun Koma Goyon Bayan Peter Obi

Kungiyar Matasa Masu Tallata Atiku Sun Sauya Sheka, Sun Koma Goyon Bayan Peter Obi

  • Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yi rashin kungiyar matasa magoya bayansa mai suna Youths for Atiku Political Group (YOFA)
  • YOFA a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata 22 ga watan Nuwamba ta ce yanzu ta koma goyon bayan Peter Obi
  • Tuni kungiyar ta sauya suna zuwa Youths for Peter Obi (YOPO) tare da bayyana cewa ta daina goyon bayan Atiku

Gabanin babban zaben 2023, kungiyar matasa magoya bayan Atiku Abubakar mai suna Youths for Atiku Political Group (YOFA) ta bayyana yin murabus daga goyon bayansa.

Matasan sun bayyana komawa tsagin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi tare da bayyana ficewa daga jam’iyyar PDP.

Wannan na zuwa ne a cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a ranar Talata 22 ga watan Nuwamba, inda tace ta raba gari da tafiyar PDP da Atiku.

Kara karanta wannan

Wike da Sauran Gwamnonin G-5 Sun Kafa Sabuwar Kungiya, Sun Ce Sam Ba Zasu Taya Atiku Kamfen Ba

Atiku ya yi rashin matasan PDP, sun koma LP
Kungiyar Matasa Masu Tallata Atiku Sun Sauya Sheka, Sun Koma Goyon Bayan Peter Obi | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa, kungiyar ta hada da taron gungun hazikan matasa a Najeriya, wadanda ke gangamin ganin matasa da mata a fannin siyasa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Zaben 202: Dalilin da yasa muka bar tsagin Atiku, bayanin kungiyar

YOFA ta ce, bayan zaben 2019, mambobin kungiyar sun yanke shawarin mayar da kujerar shugabanci zuwa Kudu kuma ta bukaci PDP ta yi hakan.

Ta ce ta yanke shawarin barin tsagin Atiku ne saboda PDP ta gaza ba ‘yan yankin Kudu tikitin takarar shugaban kasa.

YOFA ta fadi dalilin da yasa ta fara goyon bayan Peter Obi

A bangare guda, kungiyar ta bayyana goyon bayanta ga dan takarar shugaban kas ana Labour tare da sauya sunan kungiyar zuwa to Youths for Peter Obi (YOPO).

A cewar kungiyar, ta yi hakan ne saboda Peter Obi da abokin takararsa Yusuf Datti Baba-Ahmad sun kasance matasa, kwararru kuma masu jinni a jika hadi da kyawawan zukata.

Kara karanta wannan

2023: A Karshe Oshiomhole Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Tinubu Zai Kayar Da Atiku Domin Ya Ci Zaben Shugaban Kasa

Ta kuma kara da cewa, Obi da abokin gaminsa suna da duk abin da ake bukata don ganin an ciyar da kasar nan gaba tare da warware dukkan kalubale.

Peter Obi ya sha bayyana tafiya da matasa, a baya-bayan nan ya ce ba zai yi Allah wadai da kungiyar ta'addanci ta ESN ba.

Peter Obi ya ce zai tattauna da duk wasu masu fafutukar aware idan ya gaji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel