Shugabannin Kungiyar Magoya Bayan PDP Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Jihar Sokoto

Shugabannin Kungiyar Magoya Bayan PDP Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Jihar Sokoto

  • Jam'iyyar APC a jihar Sokoto ta sake samun karin mambobi yayin da wasu shugabanninta suka koma APC
  • Wata shahararriyar kungiyar goyon baya ce shugabanninta suka bayyana komawa APC saboda wasu dalilai
  • Jam'iyyun siyasa na cu ci gaba da fuskantar sauya sheka yayin da ake tunkarar babban zaben 2023 mai zuwa nan da watanni 3

Jihar Sokoto - Shugabannin wata babbar kungiyar magoya bayan PDP a jihar Sokoto sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC gabanin zaben 2023.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka ba manema labarai a jihar Sokoto daga hannun mai ba Sanata Aliyu Wammako shawari, Bashar Abubakar, Vanguard ta ruwaito.

A cewar Bashar, shugabannin kungiyar da aka fi sani da ‘Ubandoma/Sagir Youth Mobilisation and Awareness Support Group’ sun samu tarba zuwa APC daga dan takarar gwamnan jam'iyyar a zabe mai zuwa, Alhaji Ahmad Aliyu.

Kara karanta wannan

Jerin Bukatu 5 Da Kungiyar CAN Ta Gabatarwa Atiku Abubakar a Zamansu

'Yan PDP sun sauya sheka zuwa APC a Sokoto
Shugabannin Kungiyar Magoya Bayan PDP Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Jihar Sokoto | Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Alhaji Aliyu Wammaki ne shugaban jam'iyyar APC a jihar Sokoto, kuma shine sanata mai wakiltar Sokoto ta Arewa a majalisar dattawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayanin da aka gabatarwa manema labarai

A cewar sanarwar:

"Wadanda aka karba zuwa APC su ne: Lukman Kwaire da Anas Muhammad, shugaban kungiyar da sakatarenta.
"Sun kasance suna yiwa PDP aiki a bangarori da yawa amma ba su samu wata manufar siyasa ba da kuma makama a jam'iyyar wanda hakan yasa suka daina goyonta suka dawo APC.
"Sabbin mambobin sun bar APCP ne bayan da daya daga cikin masu ruwa da tsaki na APC a jihar, Alhaji Umaru Tambuwal ya shiga batun."

Bashar ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa, APC za ta yi nasara a zabe mai zuwa duba da yadda take karbar sabbin mambobi a kullum, PM News ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ganduje: Kwankwaso Bashi da Karfi Yanzu, Ba zai Kai Labari ba a 2023

Kungiyar matasan YOFA ta sauya sheka zuwa tsagin Peter Obi

A wani labarin kuma, wata kungiyar goyon baya da tallata Atiku ta matasa ta bayyana komawa tsagin dan takarar shugaban na jam'iyyar Labour, Peter Obi.

Wannan na zuwa daidai lokacin da jam'iyyun siyasa ke ci gaba da gangami gabanin zaben 2023 mai zuwa.

Kungiyar ta ce ta rasa kwarin gwiwa tun bayan da aka mika tikitin PDP zuwa yankin Arewacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel