Bayan shekaru 8, Gwamnan PDP Ya Tona Yadda Atiku Ya Wulakanta Jonathan a Zaben 2015

Bayan shekaru 8, Gwamnan PDP Ya Tona Yadda Atiku Ya Wulakanta Jonathan a Zaben 2015

  • Nyesom Wike yana ikirarin Goodluck Jonathan ba zai marawa Atiku Abubakar baya a zaben 2023 ba
  • Gwamnan na Ribas yace Atiku ya ki yarda ya goyi bayan tazarcen Jonathan duk da ya nemi taimakonsa
  • Amma Jonathan ya tallata tikitin Atiku/Obi a 2019, kuma ya nuna yana goyon bayan PDP a zaben badi

Rivers - Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, yace mutanen Atiku Abubakar sun nemi Goodluck Jonathan ya hakura da yi wa PDP takara a 2015.

The Cable ta rahoto Gwamna Nyesom Wike yana wannan jawabi wajen kaddamar da titin Akpabu-Omudioga-Egbeda, karamar hukumar Emohua, Ribas.

Kamar yadda Nyesom Wike ya fada, Jonathan ya je har Landan, yana lallashin Atiku Abubakar ya mara masa domin ya zarce a kan karagar mulki.

A lokacin tsohon mataimakin shugaban kasar ya sauya-sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC. A karshe Atiku Abubakar ya ki goyon bayan Jonathan.

Kara karanta wannan

Wike Ya Saki Sabon Bam, Ya Bayyana Yadda Atiku Ya Tozarta Jonathan a 2015

'Dan Adam da saurin mantuwa

Wike wanda yake rigima kan takarar Atiku a zaben 2023, yace mutane na da saurin mantuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Abin da ba na so da jama’a shi ne muna da sauran mantawa da tarihi. A 2015 lokacin Jonathan tana kan mulki, ya lashe zaben fitar da gwani (na PDP).
Atiku Abubakar
Atiku Abubakar da Shugabannin CAN. Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

Jonathan ya tafi Landan, ya je wani otel, Dorchester, yana rokon ‘dan takaran shugaban kasar mu na yau, Atiku Abubakar, ya dawo ya mara masa baya.
Kun san sharadin da suka ba Jonathan? Ya hakura da takararsa, ya fasa neman mulkin Najeriya. Shugaban kasa mai-ci kenan fa, aka gindayawa sharadi.

Gwamnan ya bijiro da wannan bayani ne domin ya gamsar da jama’a cewa adalci suke nema a jam’iyya da suka hakikance sai an sauke Iyorchia Ayu.

PDP take da jihar Ribas - Wike

Kara karanta wannan

Atiku Ya Hakura da Maganar Cin Zaben 2023 – Kwankwaso Ya Jero Dalilan faduwar PDP

The Nation tace tsohon Ministan kasar yana ganin cewa a dalilin abin da ya faru a wancan lokaci, Jonathan ba zai goyi bayan Atiku Abubakar a 2023 ba.

Wike ya fadawa David Umahi wanda ya gayyata wajen kaddamar da titunan cewa ka da APC ta sha wahalar yin kamfe a Ribas, domin PDP ta karbe jihar.

Hasashen zaben 2023

An gudanar da wannan bincike a kan zaben 2023, an yi hira da mutum 2000, a karshe aka fahimci 'Dan takaran LP watau Peter Obi ya fi farin jini.

Rahoto yace hasashen ya nuna ba a maganar Rabiu Musa Kwankwaso da NNPP, a Kudu maso gabas da Kudu maso Kudu, LP take da babban rinjaye.

Asali: Legit.ng

Online view pixel