Atiku Ya Hakura da Maganar Cin Zaben 2023 – Kwankwaso Ya Jero Dalilan faduwar PDP

Atiku Ya Hakura da Maganar Cin Zaben 2023 – Kwankwaso Ya Jero Dalilan faduwar PDP

  • Rabiu Musa Kwankwaso yace takarar Atiku Abubakar a zaben shekarar 2023 ba za ta je ko ina ba
  • ‘Dan takaran shugaban kasar na NNPP yace Jam’iyyar PDP ba ta da iko a jihohin da kuri’u ke da yawa
  • Kwankwaso yana ganin ba za tayi Atiku ya yi galaba a Jihohin Ribas, Kano da kuma Legas a zaben ba

Rivers - Rabiu Musa Kwankwaso mai neman zama shugaban Najeriya a karkashin jam’iyyar NNPP yana ganin Atiku Abubakar ba zai kai labari a 2023 ba.

The Nation ta rahoto Rabiu Musa Kwankwaso a ranar Litinin yace zai yi mamakin yadda PDP za ta ci zabe alhali ba ta rike da jihohin Legas, Kano da Ribas.

Tsohon Gwamnan yace ficewarsa daga jam’iyyar hamayyar ya jawo PDP ta nakasa a jihar Kano.

Haka zalika sabanin da aka samu tsakanin ‘dan takaran shugaban kasar da Gwamna mai-ci, Nyesom Wike ya sa zai yi wa PDP wahala tayi nasara a Ribas.

Kara karanta wannan

Alkawuran Atiku: Zan yiwa Arewa aiki kamar Abubakar Tafawa Balewa idan na gaji Buhari a 2023

A hasashen ‘dan takaran shugaban kasar, Atiku Abubakar ba zai iya doke APC a Legas ba, musamman idan aka yi la’kari da Bola Tinubu yana takara.

Kwankwaso ya yi wannan bayani ne a lokacin da ya kaddamar da wasu tituna a Mgbuitanwo a karamar hukumar Emohua da gwamnatin Wike ta gina.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rabiu Musa Kwankwaso
Rabiu Musa Kwankwaso tare da Nyesom Wike Hoto: @KwankwasoRM
Asali: Twitter

Jawabin Kwankwaso a Emohua

“Yanzu da Kwankwaso ya bar jam’iyyar. Wike yana fama da kan shi, kuma abububuwa suna tafiya.
Shakka babu, ba za suyi nasara a Legas ba. Sai ka fara tunani a ina za su samu kuri’un da za su ci zabe.

- Rabiu Musa Kwankwaso

Ba haka ba ne - PDP

Sakataren yada labarai na jam’iyyar PDP na kasa, Debo Ologunagba, ya maida martani tuni, inda yace babu abin da ke nuna ba za suyi nasara a jihohin ba.

Kara karanta wannan

Duk Wanda Yace 2023 Lokacinsa ne, Ya Tafka Babban Kuskure, Kwankwaso Yayi Gugar Zana

Ologunagba yana ganin babu abin da zai hana PDP karbe mulki daga hannun APC a 2023.

G5 za su yi irin abin da muka yi a 2014 - Kwankwaso

Daily Post ta rahoto Kwankwaso yana yabon Wike da sauran Gwamnonin da suka ja daga a PDP, yace irin haka 'Yan G7 suka yi a 2014, a karshe APC ta ci zabe.

‘Dan takaran shugaban kasar yana sa ran Gwamnoni biyar na PDP da suka kafa kungiyar Integrity Group za su taimaka wajen nakasa jam’iyyar hamayyar.

PDP za ta ci Jihohi 25

A baya an samu rahoto cewa Sanata Iyorchia Ayu ya ji dadin aikin da kwamitin Eyitayo Jegede suka yi har PDP ta lashe zaben Gwamna da aka yi a Osun.

A zaben Shugaban kasa da na Gwamnoni, Ayu wanda shi ne shugaban PDP, yace jam’iyyar adawa za tayi galaba a jihohi akalla 25, kuma ta karbe Aso Rock.

Kara karanta wannan

Mai Bakin Cin Rashawa Bai Isa ya Jagoranci Kamfen ba, Wike ga Shugaban PDP

Asali: Legit.ng

Online view pixel