'Yan Daba Sun Kai Wa Tawagar Atiku Abubakar Hari a Gangamin Kamfen Gombe

'Yan Daba Sun Kai Wa Tawagar Atiku Abubakar Hari a Gangamin Kamfen Gombe

  • 'Yan daban da ake kira da 'Kalare Boys' a Gombe sun farmaki magoya bayan ɗan takarar PDP, Alhaji Atiku Abubakar
  • Rahotanni sun bayyana cewa bayan tashi taron, Yan daban suka farwa mutane ta kofa mai lamba biyu a Filin wasan Pantami
  • Atiku ya riga da ya bar wurin lokacin da Yan Kalare suka kai farmakin, yan sanda sun kai ɗauki da wuri

Gombe - Aƙalla mutane uku ne suka samu raunuka ranar Litinin a wata arangama tsakanin 'yan Daban gari, Kalare Boys da magoya bayan Atiku, waɗanda suka je Gombe yakin neman zaɓe.

Punch ta tattaro cewa an yi kaca-kaca da ababen hawa huku da suka haɗa da Motar Bas, Karamar Mota da Keke Napep lokacin da Yan Daban suka mamayi mutane a Titin Filin Pantami.

Wurin kamfen Atiku a Gombe.
'Yan Daba Sun Kai Wa Tawagar Atiku Abubakar Hari a Gangamin Kamfen Gombe Hoto: Nura Nayababa/facebook
Asali: Facebook

Sakataren watsa labarai na PDP a jihar, Usman Muritala, yace ba shi da masaniya saboda ba'a sanya shi cikin masu tsara gangamin yakin neman zaɓen ba.

Kara karanta wannan

Alkawuran Atiku: Zan yiwa Arewa aiki kamar Abubakar Tafawa Balewa idan na gaji Buhari a 2023

Yace:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Bana wurin kuma na halarci filin taron ne a matsayin ɗan jam'iyya don haka na nemi wuri na zauna kamar kowa domin na kalli abinda ke wakana. Akwai matsala babba ta rabuwar kai a jam'iyya."

Meya haddasa rikicin?

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa danbarwar ta fara ne loacin da Atiku tare da 'yan tawagarsa suka fice ta Kofar mai lamba ta biyu a Filin wasan Pantami suka nufi jihar Bauchi.

'Daga nan ne Yan Kalare ɗauke da Adduna, Wukake da wasu makamai suka farwa magoya bayan PDP waɗanda ke kokarin fita daga wurin su koma gidajensu.

An ce jami'an yan sanda dake tsaron Kofa mai lamba ɗaya cikin hanzari suka kai ɗauki Kofa mai lamba biyu domin baiwa magoya bayan tsaro bayan sun koma cikin fili.

Da yawan mutanen sun tsaya cirko-cirko a cikin filin suna jiran 'yan sanda su shawo kan komai sabida 'yan kalare sun toshe hanyar zuwa Kasuwar Pantami da Gidan gwamnati suna farmakan masu wucewa.

Kara karanta wannan

Mutum 23 Sun Yanke jiki sun Fadi Yayin Tattakin Goyon Baya ga Tinubu da Shettima a Kano

Bisa tilas wasu matan PDP suka haɗa da Motar 'yan sanda ta musu rakiya domin guje wa matsala daga Yan daban Kalare, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Gombe, ASP Mahid Abubakar, yace yana cikin wata ganawa don haka ba zai iya tabbatar da abinda ya faru ba.

Kotu Ta Rushe Zaben Fidda Gwanin APC da PDP a Jihohin Arewa Biyu

A wani labarin kuma Babbar Kotun tarayya ta soke tikitin wani ɗan takarar majalisar tarayya na APC a Jigawa, ta rushe zaɓen fidda gwanin PDP a Zamfara.

Hukuncin guda biyu da Kotun ta yanke Kotun nai zama a Abuja ta yanke, ya nuna ta baiwa PDP dama ta canza zaben fidda gwanin ɗan majalisa a Zamfara.

Haka zalika Alkali ya ayyana mai shigar da ƙara a matsayin halastacceɓ ɗan takarar APC a amzaɓar Babura/Garki jihar Jigawa.

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: Wani Mutumi Ya Lakaɗa Wa Matarsa Duka Har Lahira Kan Karamin Saɓani

Asali: Legit.ng

Online view pixel