Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwanin APC da PDP a Jihohin Arewa Biyu

Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwanin APC da PDP a Jihohin Arewa Biyu

  • Babbar Kotun tarayya, Abuja ta kwace tikitin APC na takarar majalisar tarayya mai wakiltar Babura/Garki, Jigawa daga hannun Ahmad Kanta
  • Haka nan Kotun ta rushe zaɓen fidda gwanin ɗan takarar majalisar tarayya a inuqar PDP daga jihar Zamfara
  • Hukuncin biyu wanda Kotun ta yanke a lokuta da daban-daban ya shafi manyan jam'iyyu APC da PDP

Abuja - Babbar Kotun tarayya dake zama a birnin tarayya Abuja ta soke tikitin 'yan takarar mamba a majalisar wakilan tarayya guda biyu a jihohin Jigawa da Zamfara.

The Nation tace a hukunci biyu da Kotun ta yanke, ta kori Ahmad Kanta daga matsayin ɗan takarar majalisa mai wakiltar mazaɓar Babura/Garki a jihar Jigawa karkashin inuwar APC.

Alamar Kotu.
Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwanin APC da PDP a Jihohin Arewa Biyu Hoto: thenation
Asali: UGC

Haka zalika ta soke tikitin Sani Umar Ɗan Galadima, mai neman kujerar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Kauran Namoda/Birnin Magaji a jihar Zamfara a inuwar PDP.

Kara karanta wannan

Tinubi Ya Yi Gagarumin Rashi, Wani Shugaban APC da Wasu Jiga-Jigai Sun Fice Daga Jam'iyyar

Yayin da Kotun ta ayyana Alhaji Isa Dogonyaro a matsayin halastaccen ɗan takarar APC a mazaɓar Babura/Garki, Jigawa, ta kuma umarci jam'iyyar PDP ta sake zaɓe a mazaɓar Kauran Namoda/Birnin Magaji, Zamfara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Meyasa Kotun ta yanke wannan hukuncin?

Mai shari'a Inyang Ekwo, yayin da yake soke takarar Galadima na PDP a Zamfara ranar Litinin, yace ɗan Majalisar na cikin APC lokacin da jam'iyyar PDP ta gudanar da zaɓen fidda gwani.

Alƙalin yace kasancewar bai yi murabus ya sauya sheƙa daga APC zuwa PDP ba a lokacin da doka ta tanada, shi ba halastaccen mamban PDP bane kuma ba shi da ikon tsayawa takara a jam'iyyar.

Ya kafa hujja da sashi na 221 a kundin mulki 1999 da aka wa garambawul, sashi na 84 a kundin dokokin zaɓe 2022, da sashi na 50 (4) na kundin dokokin PDP ya rushe zaben fidda gwanin.

Kara karanta wannan

2023: Ganduje Ya Gaza Rufe Bakinsa Ganin Cikar Ƙwarin Matasa, Yace Tinubu Ya Gama da Kano

Dalilin soke na Jigawa

Tun farko, Mai shari'a Emeka Nwite, ya soke tikitin takarar Ahmad Kanta daga Jigawa saboda gano ya miƙa sunan ƙarya, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

A hukuncin da ya yanke ranar 10 ga watan Nuwamba, 2022, mai shari'a Emeka ya yanke cewa, Kanta wanda ya yi ikirarin sunansa Ahmed Muhammed, ya nemi takara da sunan bogi.

Yace Kanta ya bada bayanan ƙarya ga INEC don haka bai cancanci neman takarar majalisar tarayya mai wakiltar Babura/Garki ba a inuwar APC.

Sakamakon haka ya ayyana wanda ya zo na biyu kuma mai shigar da ƙara, Dogonyaro a matsayin halastaccen ɗan takarar APC a zaɓe mai zuwa.

A wani labarin kuma Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso ya amsa gayyatar gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas.

Tsohon gwamnan Kano ya isa Patakwal, babban birnin jihar Ribas kuma ya samu tarba mai kyau daga gwamna Wike yayin da zai kaddamar da wasu ayyuka a jihar.

Kara karanta wannan

Wike da Sauran Gwamnonin G-5 Sun Kafa Sabuwar Kungiya, Sun Ce Sam Ba Zasu Taya Atiku Kamfen Ba

A makon da ya gabata Wike ya gayyaci tsohon shugaban APC, Adams Oshiomhole, tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, suka kaddamar da ayyuka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel