Atiku Ya Ziyarci Gombe, Ya Sha Alwashin Farfado da Madatsar Wutar Lantarki, Zai Habaka Kasuwanci

Atiku Ya Ziyarci Gombe, Ya Sha Alwashin Farfado da Madatsar Wutar Lantarki, Zai Habaka Kasuwanci

  • Atiku ya kai ziyara jihar Gombe don tallata aniyarsa ta gaje Buhari a zaben 2023 mai zuwa, ya fadi abin da zai yiwa Gombawa
  • Ya ce zai zamewa Arewa kamar Abubakar Tafawa Balewa idan dai aka goyi bayan jam'iyyar PDP a zaben mai zuwa
  • A bangare guda, ana ci gaba da ba Atiku ciwon kai yayin da gwamnan PDP ya bayyana goyon bayansa ga dan takarar NNPP

Jihar Gombe - Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yi alkawarin tabbatar da wuta daga madatsar wuta ta Dadin Kowa da ke jihar Gombe idan aka zabe shi a zaben 2023, Guardian ta ruwaito.

A bangare guda, Atiku ya sissanta kansa da tsohon firayinministan Najeriya, marigayi Sir Abubakar Tafawa Balewa, inda yace ‘yan Arewa maso Gabas za su samu alheri idan suka zabe shi a 2023.

Kara karanta wannan

Binciken ‘Yan Sanda Ya Nuna Jihohi 2 da Za a fi Samun Tashin Hankali a Zaben 2023

Da yake magana a taron gangamin kamfen na PDP a jihar, Atiku ya ce dukkan hanyoyin da ke hada Gombe da Adamawa da Borno, da kuma hanyar da ke hada Gombe da Bauchi da Yobe duk za iyi aikin gyara su.

Alkawuran da Atiku ya daukawa Gombawa idan suka zabe shi a zaben 2023
Atiku Ya Ziyarci Gombe, Ya Sha Alwashin Farfado da Madatsar Wutar Lantarki, Zai Habaka Kasuwanci | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Dalilin da ya sa zan gyara titunan Arewa maso Gabas, daga bakin Atiku

Ya ce za iyi hakan ne don habaka alakar kasuwanci tsakanin jihohin na Arewa naso Gabashin Najeriya, jaridar Independent ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

“Bari na maimaita alkawarin da na dauka idan Allah ya sa kun goyi bayan PDP. Mun yi alkawarin karfafa ‘yan kasuwanku don inganta kasuwanci ta yadda za su fadada kasuwancinsu don matasanmu maza da mata.
“Mun kuma yi alakawarin cewa, madatsar ruwan Dadin Kowa, wanda aka gina a mulkin PDP don samar da wutar lantarki da harkar noman rani za su fara aikin samar da wuta da noman rani matukar kuka goyi bayan gwamnatin PDP.”

Kara karanta wannan

Duk Wanda Yace 2023 Lokacinsa ne, Ya Tafka Babban Kuskure, Kwankwaso Yayi Gugar Zana

“Za mu tabbatar dukkan hanyoyin da ke hada Gombe da Adamawa da Borno da Bauchi da Yobe duk an gyara su son habaka alakar kasuwanci.
“Da yawanku ba a haife ku ba lokacin da marigayi firayinminista Sir Abubakar Tafawa Balewa ya yi Mulki ba. Yanzu kuna da damar samun wani Abubakar Tafawa Balewan daga gare ni.”

A nasa bangaren, shugaban kwamitin gangamin PDP, kuma gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel y ace, tattalin arzikin zai dawo yadda yake a da kuma darajar Naira zai habaka idan aka zabi Atiku.

Yayin da Wike ke ci gaba da nuna adawa da Atiku, daya daga cikin 'yan tawagarsa ya halarci taron gangamin na Atiku a jihar Gombe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel