Kano: Mutum 23 Sun Yanke Jiki Sun Fadi a Tattakin da Aka Yi wa Tinubu/Shettima

Kano: Mutum 23 Sun Yanke Jiki Sun Fadi a Tattakin da Aka Yi wa Tinubu/Shettima

  • Rahotanni sun bayyana cewa, a kalla mutum 23 ne suka yanke jiki suka fadi a cunkoson tattakin da Kanwa suka yi don nuna goyon baya ga Tinubu
  • An fara tattakin na mutum miliyan daya ne daga fadar Sarkin Kano inda magoya bayan Tinubu da Shettima suka zarce har gidan gwamnatin jihar
  • Legit.ng Hausa ta ga yadda titin aka kawata shi kuma aka tsananta tsaro tun wurin karfe 11 na ranar Lahadin kuma ganau sun tabbatar ba a yi tarzoma a wurin ba

Kano - A kalla mutum 23 ne suka yanke jiki suka fadi a cikin jama’a da suka taru domin tattakin nuna goyon baya ga Bola Tinubu da Kashim Shettima a ranar Lahadi.

Tattakin mutum miliyan 1 wanda aka yi a Kano, ya fara ne daga fadar sarki inda aka kare shi a shatale-talen gidan gwamnati inda Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya karbe su.

Kara karanta wannan

Lokaci Yayi: Kyawawan Hotunan Kafin aure na Jaruma Halima Atete da Angonta

Tinubu ds Shettima
Kano: Mutum 23 Sun Yanke Jiki Sun Fadi a Tattakin da Aka Yi wa Tinubu/Shettima. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Tattakin ya hada da abubuwan nishadantarwa da suka hada da wasan babur, tseren dawakai, mawaka mata da maza da suka saka kayan al’adu daban-daban amma bayyane da goyon bayan APC.

Ma’aikatan tallafi da jami’an tsaro sun dage wurin tabbatar da lafiyar wadanda suka halarci wurin tare da hana cunkoson ababen hawa wanda ya cushe sassan birnin, jaridar Punch ta rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A yayin jawabi ga manema labarai, Bappa Babba-Danagundi, ya bayyana jin dadinsa kan nasarar da aka samu wurin yin tattakin inda ya kwatanta Tinubu da ‘dan takarar da Kano zasu zaba.

“Ina godiya ga Allah kan nasarar da aka samu wurin wannan taron wanda ya nuna yadda irin karbuwar da ya samu wanda ya nuna nasarar Bola Ahmed Tinubu a zaben 2023 mai gabatowa.
“A bayyane yake cewa shugabancin kasan Tinubu a Kano fararren abu ne.”

Kara karanta wannan

Rangyem: FG Ta Kara Kudi Kan Filet din Kowanne Abincin Dalibai

- Ya bayyana.

Gani ya kori ji

Kamar yadda Legit.ng Hausa ta gani a ranar Lahadi mkisalin karfe 11 na safe a daidai shata-talen gidan gwmanati, an kawata wurin da kwalliya mai launin fari, ja da bula wadanda su ne launin tutar jam'iyyar.

Hakazalika, a daidai wannan lokacin an tsananta tsaro a wurin inda Legit.ng Hausa ta ga karuwar yawan jami'an ar zuwa hanyar asibitin Abdullahi Wase wanda ke kira da asibitin Nasarawa.

Taro an tashi lafiya babu tarzoma, Matashi Abba

A zantawar da Legit.ng Hausa tayi da wasu matasa a Tarauni wadanda suka halarci taron sun bayyana cewa taro yayi kayu kuma sun yi ne saboda suna matukar goyon baya da fatan Tinubu ya haye mulkin Najeriya.

Matashi Abba Muhammad wanda ke sana'ar dinki kuma ya halarci tattakin ya bayyana cewa:

"A gaskiya taro yayi kyau kuma komai ya tafi daidai tunda ba a samu hatsaniya ko wani tashin hankali ba. 'Dan Tinubu, Seyi Tinubu ya halarci tattakin kuma Ganduje ya karbe mu a gidan gwamnati.

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaban Majalissar Dattijai Omo Ovie-Agege Yace Shine Ya Dakatar da Kudirin Tsige Shugaba Buhari

"Mutum biyu ni dai a gaban suka yanke jiki suka fadi shima kuma sakamakon cunkoso ne wai saboda hayaniya ko tashin tashina ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel