Kwankwaso: Duk Wanda Yace 2023 Lokacinsa ne, Ya Tafka Babban Kuskure

Kwankwaso: Duk Wanda Yace 2023 Lokacinsa ne, Ya Tafka Babban Kuskure

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce duk wani ‘dan takara da yace shekarar 2023 lokacinsa ne toh ya tafka babban kuskure kuwa
  • Kwankwaso yace abinda ya faru tsakanin Yar’Adua da Jonathan ne ake son ya sake maimaita kan shi a kasar nan duk da bai kama sunan kowa ba
  • Ya sha alwashin cewa ba zai janyewa kowa ba, kuma zai inganta ilimi, yaki da rashin tsaro tare da tumbatsa tattalin arziki idan yaci zabe

Legas - Sanata Rabiu Kwankwaso, ‘dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) yace duk wanda yace 2023 lokacin ne ya tafka babban kuskure.

Rabiu Kwankwaso
Kwankwaso: Duk Wanda Yace 2023 Lokacinsa ne, Ya Tafka Babban Kuskure. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Duk da Kwankwaso bai kira sunan kowanne ‘dan takara ba, yadda yayi maganar ya nuna da Asiwaju Bola Tinubu na jam’iyyar APC yake.

A yayin da ake yakin neman zaben fidda gwani, Tinubu yace ya taimaki mutane masu yawa wurin samun mukamai a gwamnati don haka wannan lokacinsa ne.

Kara karanta wannan

Mai Bakin Cin Rashawa Bai Isa ya Jagoranci Kamfen ba, Wike ga Shugaban PDP

Wannan maganar ta hau kanun labarai kuma ta dinga tashe a soshiyal midiya na tsawon lokaci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma a yayin jawabi a Legas ranar Lahadi, Kwankwaso yace zaben 2023 zai kasance na daban, Daily Trust ta rahoto.

Ya kara da kira ga ‘yan Najeriya kan kada su zabi ‘dan takarar da bashi da lafiya inda ya zargi cewa wasu suna son zama shugaban kasa ta hanyar da Goodluck Jonathan ya zama bayan mutuwar shugaba Umaru Musa Yar’Adua.

“Jama’a yanzu basu batun jam’iyya, batun ‘yan takara suke da mutane. APC da PDP duk sun gaza. Saboda haka ne muke cikin halin da muke ciki a yau.
“Na shirya muhawara. Mu saka katikan mu a teburi. Wasu daga cikin ‘yan takarar suna gudun muhawarar. Wasu su kalla kansu a madubi kuma su fada mana gaskiya.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Wasu Gwamnoni Sun Kama Hanyar Ficewa Daga PDP? Atiku Ya Yi Magana

“Wasu sun girme mana. Ba ku isa ku boye hakan ba. Duk wanda yace 2023 lokacinsa ne ya tafka babban kuskure.”
“A 2007, Yar’Adua ya zama ‘dan takarar PDP bayan an gama tuntubar jama’a. Amma ba a yi bincike mai kyau ba. Mun san abubuwa amma ba a tambaye mu ba kuma muka shiga wani hali saboda rashin lafiya Umaru.
“A yau, irin wannan abun ne ke faruwa. Wasu na tunanin daga zama mataimakin shugaban kasa zasu zama shugaban kasa babu dadewa.”

- Yace.

Vanguard ta rahoto cewa, Kwankwaso ya kara da shan alwashin cewa ba zai janyewa kowa ba, inda ya kara bayyana yadda yayi niyyar yakar rashin tsaro, tumbatsa tattalin arziki da inganta ilimi idan aka zabe shi.

Afenifere: Tsagin kungiyar Yarabawa tayi wa Kwankwaso mubaya’a

A labari na daban, Sanata Kwankwaso ya ziyarci Legas inda aka samu baraka a kungiyar Yarabawa ta Afenifere.

Wani tsaginta sun ce Bola Tinubu suke baya yayin da wani tsagin suka ce Kwankwaso suke yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel