Aisha Buhari Ta Rangada Lalle na Musamman Mai Nuna 'Dan Takaranta a 2023

Aisha Buhari Ta Rangada Lalle na Musamman Mai Nuna 'Dan Takaranta a 2023

  • Aisha Muhammadu Buhari ta dage wajen yi wa Bola Tinubu da Kashim Shettima kamfe a zaben 2023
  • A matsayin Uwargidar Shugaban kasa, Aisha Buhari tana jagorantar kwamitin mata da matasa a APC
  • Mai dakin shugaban Najeriyan tayi lallen da yake nuna tana goyon bayan takarar Bola Tinubu 100%

Abuja - Uwargidar shugaban Najeriya, Aisha Muhammadu Buhari tayi kira ga duk ‘yan jam’iyyar APC suyi wa takarar Tinubu/Shettima aiki a zabe.

Hukumar dillacin labarai na kasa tace Aisha Muhammadu Buhari ta kaddamar da sashen mata da matasa na yakin neman zaben Tinubu/Shettima.

Mai dakin shugaban kasar ta kaddamar da kamfen a ranar Alhamis a Ilorin, jihar Kwara.

Aisha Buhari tace jam’iyyar APC tayi amfani da salon yakin neman takara na dabam a zabukan 2015 da 2019, kuma za a sake yin irin hakan a 2023.

Kara karanta wannan

APC ta Fito Dabarar Da Za Tayi Amfani Wajen Ganin Tinubu Ya Doke PDP da LP - Saraki

A maimaita kokarin baya - Aisha Buhari

Matar Mai girma Muhammadu Buhari tayi kira ga mata da kuma matasa da suyi amfani da irin kokarin da suka yi a baya, wajen ganin nasarar APC.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahoton yace matar shugaban kasar ta mika tutar jam’iyya ga uwargidar ‘dan takara, Oluremi Tinubu wanda a yanzu Sanata ce mai wakiltar jihar Legas.

Aisha Buhari
Aisha Buhari da Bola Tinubu Hoto: Aisha Muhammadu Buhari
Asali: Facebook

Mai dakin ‘dan takaran mataimakin shugaban kasa, Nana Kashim Shettima ta halarci gangamin.

Ana haka sai ga rahoton hotuna da bidiyo na yawo, an ga Mai dakin shugaban kasar ta rangada lalle a hannuwa mai dauke da tambarin Bola Tinubu.

Wata kungiya ta magoya bayan Gwamnan Legas a shafin Twitter¸@JideSGroup ta wallafa bidiyonta tana nuna wannan kunshi da tayi a tafukanta.

Lallen zane ne na irin hular da Tinubu yake sa wa, wanda wannan tambarin shi ne a siyasa.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Ya Sa Arewa Ke Goyon Bayan Tinubu, Sanata Mai Karfin Fada A Ji A APC Ya Magantu

Da yake magana a shafinsa na Twitter, Festus Keyamo wanda shi ne kakakin kwamitin yakin zaben APC, ya jinjinawa uwargidar shugaban kasar.

“Uwargidar Najeriya, Aisha Buhari tana bakin aiki daga fagen daga. Gaskiya tana bayyana ga abokan adawarmu.”

- Festus Keyamo

Za ayi amfani da manoma a ci zabe

Domin ganin Bola Tinubu ya ci zaben 2023, an ji labari cewa kwamitin yakin neman zabe zai yi amfani da manoma da ‘yan kasuwan Arewacin Najeriya

Shugaban sashen kasuwanci da tattalin arziki na kwamitin takaran APC, Gbemisola Ruqayyah Saraki tayi wannan bayani a taron da suka shirya a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel