Dalilin Da Ya Sa Arewa Ke Goyon Bayan Tinubu, Sanata Mai Karfin Fada A Ji A APC Ya Magantu

Dalilin Da Ya Sa Arewa Ke Goyon Bayan Tinubu, Sanata Mai Karfin Fada A Ji A APC Ya Magantu

  • Takarar Asiwaju Bola Tinubu dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ta samu tagomashi daga arewacin Najeriya
  • A yayin da babbannzaben shekarar 2023 ke karatowa, mutanen Zamfara sun sake goyon bayan takarar Tinubu yayin da suke cewa yana da gaskiya da amana tsakanin yan takarar
  • Sanata Kabiru Marafa, jagoran kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC ga gwamnan jihar za su cigaba da yi wa Tinubu kamfen gabanin zaben 2023

Zamfara - Shugaban kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, PCC, a Zamfara ya ce masu ruwa da tsaki a jihar suna goyon bayan Asiwaju Bola Tinubu saboda gaskiyarsa da adalci da rikon amana.

Ya bayyana hakan ne cikin sanarwa da ya fitar a Gusau a ranar Alhamis 17 ga watan Nuwamba ta bakin sakataren watsa labarai na APC, Malam Yusfu Idris, Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zaɓen Shugaban Ƙasa Na 2023: Jerin Buƙatun Da Shugabannin CAN Suka Gabatarwa Tinubu A Abuja

Tinubu da APC
Dalilin Da Yasa Arewa Take Goyon Bayan Tinubu, Sanata Mai Karfin Fada A Ji A APC Ya Yi Magana. Hoto: @OfficialBAT
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jigon APC ya yi magana kan dalilin da yasa Arewa ke goyon bayan Tinubu

Marafa, a wurin taron da kungiyoyin unguwanni, ya yi magana kan bukatar cigaba da tattaunawa kan cancanta da iya aiki na dan takarar na APC, The Nation ta kara.

Idris ya ce:

"Shugabannin PCC na Zamfara karkashin jagirancin Sanata Marafa, na cigaba da tattaro wa Sanata Tinubu magoya baya da Gwamna Matawalle, da yan takarar APC a babban zaben 2023.
"Shugabannin unguwanni da dama sun halarci taron da ka yi a gidan gwamnatin jihar Zamfara da ke Gusau."

Marafa ya aika sako ga shugabannin jam;iyyar APC a yan Najeriya

A cewar sanarwar, Marafa ya yi kira ga shugabannin unguwanni su goyi bayan Tinubu saboda adalcinsa, gaskiya, amintaka da rikon amana, yana mai cewa shi mutum ne mai tsoron Allah.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Yasa Na Zabi Shettima Musulmi Dan Uwana, Tinubu Ya Yiwa CAN Bayani

Sanarwar ta kara da cewa:

"Ya nemi goyon bayansu don hada kan masu zabe, musamman a wuraren taruwa, don su zabi yan takarar APC.
"A matsayinku na shugabanni da ke kusa da mutane, ana matukar girmama kuma galibi mutanen ku na jin maganan ku.
"Takarar Tinubu da Shettima zai kawo cigaba mai dorewa, daga tattalin arziki, inganta tsaro, samar da arziki tsakanin mutanen."

Marafa ya yi kira ga mutanen su yi addu'ar dawowar zaman lafiya a jihar.

aDalilin Da Yasa Arewa Take Goyon Bayan Tinubu, Sanata Mai Karfin Fada A Ji A APC Ya Yi Magana, Ya Fada Dalili Mai Muhimmanci.

Zaɓen Shugaban Ƙasa Na 2023: Jerin Buƙatun Da Shugabannin CAN Suka Gabatarwa Tinubu A Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ya gana da shugabannin kungiyar kiristocin Najeriya, CAN, a Abuja.

Kara karanta wannan

An gamu: Tinubu ya gana da CAN kan muradai da buktun Kiristocin Najeriya

CAN tunda farko ta nuna cewa ba ta goyon bayan tikitin musulmi na musulmi na jam'iyyar APC ta yi bayan zaben Kashim Shettima, tsohon gwamnan jihar Borno a matsayin abokin takararsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel