APC ta Fito Dabarar Da Za Tayi Amfani Wajen Ganin Tinubu Ya Doke PDP da LP - Saraki

APC ta Fito Dabarar Da Za Tayi Amfani Wajen Ganin Tinubu Ya Doke PDP da LP - Saraki

  • Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC zai yi amfani da manoma da ‘yan kasuwa a Arewa
  • Gbemisola Ruqayyah Saraki tayi wannan bayani da ta kaddamar da kwamitin kasuwanci a takarar APC
  • Jam’iyyar APC tana kokarin ganin Bola Ahmed Tinubu ya doke sauran ‘yan takaran hamayya a 2023

Abuja - Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya fito da tsare-tsare da zai bi wajen ganin nasarar Bola Ahmed Tinubu a 2023.

Wani rahoto da muka samu daga Daily Trust a ranar Juma’a, 18 ga watan Nuwamba 2022, ya nuna APC za tayi aiki da manoman da ke Arewacin Najeriya.

Jam’iyya mai mulki za tayi amfani da sauran ‘yan kasuwan da ke jihohin Arewa wajen ganin Bola Tinubu ya yi galaba a zaben shugaban kasa da za ayi.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Ya Sa Arewa Ke Goyon Bayan Tinubu, Sanata Mai Karfin Fada A Ji A APC Ya Magantu

Sanata Gbemisola Ruqayyah Saraki tayi wannan bayani a lokacin da ta kaddamar da ‘yan kwamitinta na bangaren kasuwanci da tattalin arziki a makon nan.

Ministar tarayyar ce take jagorantar wannan kwamiti a majalisar yakin neman zaben shugaban kasa.

Da take bayani a garin Abuja, Gbemisola Ruqayyah Saraki ta shaidawa kwamitinta mai mutum 96 cewa za ayi amfani da ‘yan kasuwa wajen lashe zabe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bola Tinubu
Bola Tinubu da magoya bayan APC Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Kokarin da aka yi a lokacin COVID-19

Gbemisola Saraki tace tattalin arzikin Duniya ya galabaita a sakamakon annobar COVID-19, amma duk da haka gwamnatin Najeriya ta rage radadin sosai.

Ministar take cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta taimakawa mutane da kudi da sauran abubuwa da ake bukata domin a iya samun saukin annobar.

Gidan rediyon Najeriya ya rahoto ‘yar siyasar tana cewa an umarce su suyi amfani da wannan dama wajen wayar da kan kungiyoyin ‘yan kasuwa a Arewa.

Kara karanta wannan

Manyan Kudu maso Kudu Sun Fara Shirye-Shiryen Karya Bola Tinubu a Zaben 2023

Jam’iyyar APC za tayi wa ‘yan kasuwan da suke yankin alkawarin kawo tsare-tsare da manufofi da za su taimaka masu idan Tinubu ya karbi mulki a 2023.

Tsohon gwamnan na Legas zai gwabza da Atiku Abubakar, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso masu neman takarar shugaban kasa a PDP, LP da NNPP.

Dalilin dauko Shettima

An ji labari shugaban All Progressives Congress (APC) Rebirth Group yace ayyukan Kashim Shettima a lokacin yana Gwamna suka jawo ya samu takara.

Aliyu Audu yace Sanata Shettima ya yi abin a-yaba a bangaren ilmi da kiwon lafiya a lokacin da ya yi Gwamnan Borno, don haka BolaTinubu ya dauko shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel