Gwamnan Lalong Ya Ce a Jos Aka Zabi Buhari, Don Haka Aka Bude Kamfen Din Tinubu a Can

Gwamnan Lalong Ya Ce a Jos Aka Zabi Buhari, Don Haka Aka Bude Kamfen Din Tinubu a Can

  • Gwamna Simon Lalong na jihar Filato ya bayyana dalilin da yasa jam'iyyar APC ta zabi jiharsa don kaddamar da gangamin kamfen dinta
  • Ya kuma tuna da tarihin shekaru 30 da suka shude da irin nasarar da Jos ta samar, da kuma hangensa na zaben 2023
  • A yau ne 15 ga watan Nuwamba jam'iyyar APC ta fara gangamin kamfen dinta a birnin Jos, Arewa ta Tsakiya a Najeriya

Jos, Filato - Darakta janar na tawagar gangamin neman zaben APC kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya bayyana ainihin dalilin da yasa shugabancin APC ta zabi jihar a matsayin wurin bude kamfen din Tinubu gabanin 2023.

Legit.ng ta tattaro cewa, ya bayyana hakan ne a filin wasa na Rwang Pam da ke birnin Jos a jihar, inda aka bude gangamin kamfen na dan takarar shugaban kasan AOC, Bola Ahmad Tinubu.

Ya ce APC ta zabi Jos ne duk da kasancewarta jihar Kiristoci saboda a nan ne aka zabi shugaban Buhari ya hau mulki a zaben da ya dare kujerar shugaban kasa.

Simon Lalong ya fadi dalilin da yasa APC ta zabi Jos don fara kamfen
Gwamnan Lalong Ya Ce a Jos Aka Zabi Buhari, Don Haka Aka Bude Kamfen Din Tinubu a Can | Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

A Jos aka kaddamar da kamfen na MKO Abiola, inji gwamna Lalong

Hakazalika, gwamnan ya kuma tuna da yadda dan yankin Kudu maso Yamma ya zo Jos a baya kuma ya yi nasara, ga shi yanzu tarihi ya maimaita kansa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalaman Lalong:

"Jos na da dimbin tarihi. A nan ne Jos marigayi MKO Abiola daga yankin Kudu maso Yamma ya zama dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar SDP tare da abokin takararsa daga Arewa maso Gabas, kuma ma mutumin Kanuri daga jihar Borno.
"Bayan shekaru 30, wani mutum daga Kudu maso Yamma ya zabi abokin gaminsa daga Arewa maso Gabas kuma Kanuri, wannan na nufin tarihi zai maimaita kansa wannan yasa muka fara kamfen din a Jos.

"Mun kagu mu samu Asiwaju Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa na gaba. Za mu samu sama da 2/3 na sanatoci da mambobin majalisar tarayya."

Su Buhari sun tattara a Jos, an fara gangamin kamfen Tinubu

A tun farko kun ji cewa, tawagar kamfen dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ta tattara zuwa jihar Filato domin bude kamfen na farko a can.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da sauran jiga-jigan APC ne suka halarci wannan taro mai dimbin tarihi a birnin Jos.

Asali: Legit.ng

Online view pixel