2023: Gwamnan Arewa Mai Ƙarfin Iko Ya Bada Hutun Aiki Yayin Da Buhari, Tinubu Suke Ƙaddamar Da Kamfen Din APC

2023: Gwamnan Arewa Mai Ƙarfin Iko Ya Bada Hutun Aiki Yayin Da Buhari, Tinubu Suke Ƙaddamar Da Kamfen Din APC

  • Simon Lalong, gwamnan jihar Filato, ya ayyana Talata a matsayin ranar hutu ga ma'aikata don kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na APC
  • Lalong, wanda shine shugaban kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi jihar a ranar Talata da safe don kaddamar da kamfen din
  • A sanarwar, ya ce za a samu cinkoson ababen hawa saboda ziyarar shugaban kasar, don haka, aka bawa ma'aikata hutu don sawwake musu shiga damuwa

Jos, Filato - Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya ayyana ranar Talata, 15 ga watan Nuwamba a matsayin ranar hutu a dukkan jihar saboda ziyarar Shugaba Muhammadu Buhari, Bola Tinubu da wasu shugabannin jam'iyyar APC.

Hakan na cikn wata takarda ne mai dauke da sa hannun kwamishinan labarai na jihar, Dan Manjang, da aka fitar a ranar Litinin 14 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Tinubu Ya Nuna Bajintarsa Ta Rawar Da Ba A Saba Gani Ba Yayin Da APC Ta Kaddamar Da Kamfen A Filato

Gwamna Lalong
2023: Gwamnan Arewa Mai Iko Ya Bada Hutun Aiki Yayin da Buhari, Tinubu Suke Kaddamar Da Kamfen Din APC. Hoto: Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Na APC.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

APC za ta kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa

Gwamna Lalong shine shugaban kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na APC.

Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC ta wallafa wannan sanarwar a shafinta na Tuwita a ranar Talata da safe.

Shugaban kasa da wasu jiga-jigan jam'iyyar mai mulki sun isa jihar don kaddamar da yakin neman zanen shugaban kasa na APC ta zaben 2023.

Sanarwar ta kara da cewa an bada hutu ga ma'aikata ne saboda ana tsamanin samun cinkoson ababen hawa saboda ziyarar Buhari da sauran shugabannin APC zuwa jihar.

Abin da ke faruwa da APC, Simon Lalong, Muhammadu Buhari da Bola Tinubu a baya-bayan nan

A cewar jihar, ana sa ran shugaban kasar zai kaddamar da yakin neman zaben dan takarar shugaban kasar na APC a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP a Kudu ya gayyaci sarkin Kano, Buhari da saruan jiga-jigai don kaddamar aiki a jiharsa

Wani sashi na sanarwar ta ce:

"Ana sa ran shugaban kasa zai kaddamar da yakin neman zabe a filin motsa jiki na Rwang Pam da ke Jos, misalin karfe 10 na safe a ranar."

Karanta cikaken sanarwar a nan.

Melaye, Keyamo Sun Yi Wa Peter Obi Izgili A Yayin Da Magoya Bayansa Ke Faɗa Akan Rabon Kuɗi

Festus Keyamo, mai magana da yawun kwamitin kamfen din dan takarar shugaban kasa na APC, da Sanata Dino Melaye, kakakin kwamitin yakin neman zabe na dan takarar shugaban kasa na PDP, sun yi wa Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na Labour Party izgili, kan bidiyon magoya bayansa da ke fada da juna, Daily Trust ta rahoto.

A wasu bidiyon da ke yawo a dandalin sada zumunta, an ga wasu mutane suna zanga-zangar cewa ba su samu kasonsu da aka musu alkawari ba saboda halartar babban taron Labour Party a jihar Abia.

Kara karanta wannan

2023: Kada Yan Najeriya Su Cire Rai, APC Zata Kawo Canjin da Suke Bukata, Tinubu

Asali: Legit.ng

Online view pixel